Connect with us

MAKALAR YAU

Harin ’Yan Bindiga: Wane Hali ’Yan Gudun Hijirar Faskari 3,700 Ke Ciki? (2)

Published

on

Kamar yadda na ambata a satin da ya gabata cewa wannan labari na ban tausayi da halin da ‘yan gudun Hijirar Faskari su ka samu kansu sakamakon hare-haren ‘yan bindiga bai kare ba, cikin ikon Allah yau za mu cigaba.

Daga jin yadda labarin ya fara lallai kasan bala’in ‘yan bindiga ya wuce yadda ake tunani musamman idan har hukumomin tsaro suka yi shakulatan bangaro da wannan lamari, dole ne a cigaba da shiga cikin matsatsin rayuwa.

Kadda a manta fiye da mutane 4,000 ne ‘yan bindiga suka yiwa sanadiyar rabawa da muhalinsu kuma mata ne da kananan yara babu magidanci acikin su, sannan da yawan mazajen an kashe su wasu kuma sun tsira da rayuwarsu amma har yanzu ba su sake haduwa da iyalansu ba.

Haka kuma idan muka yi la’akari da yanayin kula da lafiyar wadannan mutane shi ma abu ne da ke bukatar bin didigi domin ganin halin da suke cikin da kuma abinda ya shafi lafiyarsu.

Kazalika mun bayyana yadda gwamnan jihar Kasina Alhaji Aminu Bello Masari tare da wasu ‘yan kisihin kasa suke taimakawa wadannan ‘yan gudun hijira shi ma abin a yaba ne , sannan a duba a ga cewa taimakon yana isa ga wadanda aka bada domin su ko kuwa ya bi ta hanyar da taimakon Korona ke bi?

Kamar yadda muka ambata cewa gwamna Masari yana amfani da kudadan aljihunsa wajan taimakawa wadannan mutane domin tausayawa, haka bai hana shi yin tataki ba domin yin ta’aziyar wadanda suka rasa rayuwarsu tare da yin jaje ga wadanda suka samu raunuka kuma ya gana da wadannan ‘yan gudun Hijira da ke Faskari da kuma Dandume.

Ziyarar dai ta kasance kamar ta ban hakuri ga al’ummomin kananan hukumomin Faskari da Dandume wadanda ‘yan ta’adda suka kai ma hari na babu gaira babu dalili wanda yayi sanadiyyar mutane sama da Saba’in suka mutu (70).

Gwamnan wanda ya fara wannan ziyara da sansanin ‘yan gudun hijira da ke a makarantar firamare ta gwaji (Pilot) da ke cikin garin Faskari, ya tausaya tare da kuma jajanta wa al’umma baki daya. Ya kuma yi kira gare su da cewa su dauki wannan ibtila’i a matsayin kaddara wadda ba za a iya kaucemawa ba, duk da cewa kuma yin hakan ko kadan ba zai dauke nauyin da ya rataya a kan Shuwagabanni na tsaron lafiyar su da dukiyoyin su ba.

Gwamnan ya bayyana cewa ya san al’umma suna kuka da hawayen su kan wannan al’amari, to amma shi a kullum yana kwana da tashi a cikin tashin hankalin sanin cewa gobe kiyama sai Allah zai tambaye kan wadannan da ma sauran al’amurra da suka shafi al’ummar wannan jiha ta Katsina.

Alhaji Aminu Bello Masari ya roki al’umma da suyi hakuri kuma su daure suyi afuwa kan wannan mummunan lamari marar dadi domin Allah na shaida ba rungume hannuwa sukai suna kallo ba, a’a, suna kan kokarin su wadannan matsaloli suke afkuwa.

Gwamna Masari ya kara da cewa kokarin da suke tayi wajen kawo karshen matsalar yasa yanzu haka Sojoji sun canza salo da taku na kawo karshen wannan asarar rayuka da dukiyoyi da ake tayi.

Haka kuma, rundunar Sojojin kasa ta kasar nan za ta gudanar da bikin ta na shekara shekara a Faskari kuma za su ragade dajin nan kaf din shi domin tabbatar da ba a bar ko da dan ta’adda guda ba wanda zai hana al’umma zaman lafiya.

Ya kuma yi kira ga al’umma da suci gaba da addu’o’in samun zaman lafiya da jagoranci na kwarai daga Shuwagabanni tare kuma da ba jami’an tsaro goyon baya, musamman ta bangaren bada sahihan bayanai da za su taimaka wajen ganowa da durkusar da ‘yan ta’adda.

Sai dai duk da irin wannan tausayawa da tattakin domin yin jaje da ta’aziya ga wadannan mutane jama’ar wannan yanki na kokawa da dan majalisar Dattawan yankin wanda suka yi zargin ya kyale s ba tare da koda yi masu jaje ba.

Tabbatacen zance ya fito daga bakin mataimakin shugaban jam’iyyar APC na yankin Funtua Alhaji Bala Abu Musawa inda ya bayyana cewa Sanata Bello Mandiya ya kauracewa wadannan mutane da suke bukatar taimakonsa a irin wannan yanayi da suka shiga na matsala.

Bala Abu Musawa yana wannan magana ne a dai dai lokacin da ‘yan gudun Hijira mutun 3,700 wanda yawaicin su mata ne da kananan yara ke neman taimako a wata firamari da ke Faskari.

Rahotanni sun bayyana irin gudunmawar da gwamnatin jihar Katsina da kuma shuwagabanin kananan hukumomin da ‘yan siyasa da masu hannu da shuni suka bada domin tallafawa wadannan baynin Allah su samun saukin rayuwa

Sai dai mataimakin shugaban jam’iyyar na cewa ya kamata Sanata Mandiya ya dawo ya san halin da mutanen shi ke ciki, ya kuma tausaya masu da taimaka masu kamar yadda wanda ya gada Sanata Abu Ibrahim ke yi lokacin da yake rike da wannan matsayin.

Alhaji Bala Abu Musawa ya kara da cewa shi dai a iyakar saninsa da kuma ofis din shi baya da wata masaniya, game da wani taimakon da Sanata Bello Mandoya ya badako ya aiko wani, ya ce haryanzu babu wani sako da ya sameshi balanta a rabawa mabukata da ke wannan sansani na ‘yan gudun Hijira da ke Faskari

Kazalika mutanen yankin Funtua sun bayyana takaicinsu tare da nadamar zaben da suka yi wa Sanata Bello Mandiya a shiyyar Funtua, wanda bincike ya tabbatar da cewa babu wani tallafi ko Jaje balanta na gudummuwa daga Sanata Bello Mandiya

Mazauna wajen sun bayyana yadda masu rike da mukaman siyasa na yankin ke taimaka masu, misali Alhaji Bashir Ruwan Godiya mai ba gwamnan Katsina shawara akan harkar ilmi mai zurfi da kwamishinnan muhalli da dan majalisar jiha mai wakiltar su dama uwa uba gwamnan na Katsina duk suna tallafawa halin da suke ciki.

Sai dai duk da wannan korafi na mutanen wannan yankin, yasa an tuntubi Sanata Bello Mandiya domin jin ba’asin sa gane da wannan korafi ta hanyar buga waya da aika sakon kar ta kwana a wayarsa, don jin ta bakinsa, sai dai kash ba a samu nasarar hakan ba. Haka kuma mun yi kokarin jin ko yana da masu tafiyar da harkokinsa shima shiru kaki ji kamar an tura Bello Mandiya Sanatan Yankin Funtua

Muna sane da irin harinta’addacin da ‘yan bindiga suka kai karkashin wani dan ta’ada mia suna Adamu Aleiro ‘yankuza da sunan daukar fansa a garin Kadisau da ke karamar hukumar Faskari inda sama da mutane 70 suka rasa rayukansu, wannan yasa gwamna Masari tare da mukaraban gwamnatinsa suka kai ziyara ta’aziya da jaje a wannan gari.

A cikin wannan tawaga akwai mataimakin gwamna, Alhaji Mannir Yakubu da Sakataren gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, da mataimakin Shugaban Majalisar Dokoki ta jiha Injiniya Shehu Dalhatu Tafoki, Kwamishinan Kula da Muhalli Alhaji Hamza Suleiman Faskari, Mai ba Gwamna Shawara a kan Ilimi Mai Zurfi Kwamared Muhammad Bashir Ruwan Godiya da sauran manyan jami’an Gwamnatin Jiha.

Yanzu haka an kafa wani kwamitin mai karfin gasle wanda zai taimaka wajan raba kayayykin tallafi ga wadannan ‘yan gudun Hijira a karkashin kwamishin wassani, jin dadi da walwalar jama’a Honorable Sani Aliyu Danlami domin tabbatar da wannna sakon isa ga wadanda aka bada domin su.

Sannan gwamna Masari ya yi wata magana mai tayar da hankali a lokacin kaddamar da wannan kwamitin inda ya ce “Wadannan kayayyaki dai na masu iftula’i ne, duk wanda iftula’i bai sama ba yaci su, to tabbas shima ya jira iftila’i zai zo ya iske shi bada jimawa ba Insha Allahu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: