Harin ‘Yan Bindiga: ‘Yan Sanda Sun Bazama Neman Shugaban Yagba Ta Yamma

Harin

Daga Ahmed Muh’d Danasabe,

Rundunar ‘yan sanda a Jihar Kogi ta bazama neman shugaban shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Hon Pious Kolawole ruwa a jallo, wanda ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka yi garkuwa da shi a yayin da suka kai masa hari a garin Eruku da ke jihar Kogi.
Mai magana da yawun rundunar, DSP William Aya ne ya furta hakan ga manema labarai  a jiya lahadi, yayin da yake tabbatar da kai harin kan Kolawole da kuma wani kwamishina a hukumar kula da fensho na Jihar Kogi, Mista Solomon  Akeweje wanda Allah yayi wa rasuwa a sakamakon harin yan bindigan.
DSP Aya yace Hon Pious Kolawole da marigayi Akeweje,  suna kan hanyarsu ne ta dawo wa daga Ilori, babban birnin Jihar Kwara zuwa garin Egbe dake Jihar Kogi a yayin da yan bindigan suka kai musu hari a garin Eruku, waddagari ce data yi iyaka da jihohin biyu.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan ya yi bayanin cewa yan bindigan sun harbi Mista Akeweje, inda nan take yace ga garinku nan, inda ya kara da cewa a yanzu an ajiye gawarsa a asibitin ECWA dake Egbe, a yayin da kuma rundunar ta shiga neman shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Hon Pious Kolawole ruwa a jallo, wanda kawo lokacin hada wannan rehotu, ba a san inda yake ba, a sakamakon kai harin na yan bindigan.
Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kogi, Mista Ede Ayuba ya tura jami’an ‘yan sanda zuwa yankin domin nema da kuma kubutar da shugaban karamar hukumar daga hannun wadanda ake zargin sunyi garkuwa da shi,inda har ma ya jaddada cewa rundunar ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kubutar da shi, kamar yadda DSP Aya ya bada tabbaci.

Exit mobile version