Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Harkar Lafiya Na Bukatar Taimako A Nijeriya –Dr. Popoola Margret

by
3 years ago
in TATTAUNAWA
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

A cikin satin da ya gabata ne shugabar sashen zartarwa na cibiyar kimiyar lafiya da a ke kira Centre For Health Education and Life Promotion (C-HELP) ta shirya taron kara wa juna sani kan kalubalen da harkar lafiya da marasa lafiyan ke ciki a kasa bakidaya. Taron ya sami halartar kwararru likitoci da masana bangare daban-daban a fadin Nijeriya ciki har da shugaban asibitin kwararru na Jihar Kano, wato Dakta Waziri Garba Dahiru da Farfesa Umar Ibrahim, wadanda duk sun gabarar da mukala daban-daban da ke nuna kalubalen da harkar lafiya ke ciki da matsalar da ke sa a ke fita da marasa lafiya kasar waje waje neman magani al’halin akwai kwararrun masana a gida Nigeriya. Bugu da kari cibiyar ta gaoyyato marasa kafiya na bangarori da dama don su bayyana wa jama’a kalubalen da suke fuskanta a halin da suke ciki.

A rana ta biyu ne wakilin LEADERSHIP A YAU, ISA ABDULLAHI, ya nemi jin ta bakin shugabar kungiyar, DAKTA POPOOLA MARGRET, game da dalilin shirya wannan taro. Ga kuma yadda wannan tattauna tasu ta kasance da ita:

Mene ne dalilin shirya wannan taro?

Labarai Masu Nasaba

2023: Yayin Da APC Da PDP Suka Yi Jadawali…

Abin Da Ya Sa Muka Ce A Rika Gwajin Shaye-shaye Kafin Aure – Buba Marwa

Wannan taron an shirya shi ne domin akwai bukatar mu waiwayi sashen lafiya a Nijeriya, mu kalli matsalolinsa da muke da su mu kuma bullo da hanyoyin da suka dace domin kawo gyara, gyaran da zai iya ciyar da mu gaba a bangaren lafiya ga mutanenmu. Abin bakin ciki ne a ce cututtuka da dama suna samun mutanenmu, muna da kwararrun malaman asibiti, malaman asibitin Nijeriya sun sai aikinsu sosai. Idan sun fita kasashen waje suna aiki mai kyau, amma a gida ba mu iya yi, muna da bukatar kayan aiki domin mu gudanar da aikinmu ga marasa lafiya, a wasu lokutan marasa lafiya sai dai a basu zabin irin aikin da za a yi musu kuma su marasa lafiyan basu da kudin. Dan haka muna bukatar gwamnati ta shigo ta dauki nauyin wasu magungunan ga marasa lafiya, gwamnati na kokari amma akwai sauran aiki. Muna murna cewa yanzu NGIS za ta dauki nauyin wasu magungunan da wasu ayyukan tiyata, wannan abin murna ne. Muna fatan wannan zai kasance ba wai kawai a takarda ba domin marasa lafiya su amfana. Dan haka akwai abubuwa da yawa da likitocin Nijeriya za su iya yi amma ba za su iya ba saboda basuda yanayin yin hakan mai kyau, ga rashin kudi. Muna kuma bukatar mu rika yin bincike-bincike, ana ta kirkire-kirkire a duniya, musamman a duniyar likitanci amma muna a baya, ba ma yin bincike-binciken da zai haifar da mafita a al’amurra, muna so mu canza haka a bangaren lafiya, mu fara yin bincike-binciken da za su sa mutanenmu su samu cigaba, su iya kirkiro abubuwa, muna so mutanensu su bada karfi sosai wajen bincike-bincike. Su kasance masu yin nazari a cikin bincikensu, ba wai kawai a tattaro bayanai marasa amfani baa rubuta a takarda, wannan ba ya haifar da mafita a dimbin al’ummar mu. Muna son binciken da in an yi shi kuma sakamakonsa ya fito zai haifar da mafita ga al’ummar Nijeriya, muna son kasancewa kasar da ake zuwa domin neman lafiya, muna so mutanenmu su daina fita waje domin neman lafiya, muna so mutanenmu su samu kwarin gwiwa su kuma samu kulawar lafiyar da suke bukata a nan Nijeriya, muna so mutane daga zagayen Afirka su zo Nijeriya su nemi lafiya kuma su same ta, wannan shine aniyar mu, zai iya kasancewa an fara kadan kadan amma muna da manufa kuma mun san inda muka dosa kuma za mu yi hakan.

ADVERTISEMENT

To ko menene abinda aka cimmawa a taron?

An samu farin ciki sosai, na yi murna, ni ba shirya taron amma na karu sosai, a yayin da ka saurari bayanai daga farfesoshi, daga bakin manyan Daktoci kamar Dakota Akuse, mutane kamar Oyinda Olajonse, mutane kamar Henry Wanda ya zo tun daga Port Harcourt, in ka hada manyan mutane a waje kasan yadda abin ya ke, saboda haka na karu sosai dalilin taron.

Shin wannan kungiya na da wani sako ga mahalartan?

Sai Dakta Popoola tace tabbas, ina son yin godiya ba mahalartan domin daukar lokacinsu da suka yi da kasancewa a nan, na san sun karu sosai, ina so su yada abinda suka koya ta yadda za su kai hasken al’ummunsu. Ko kai likita ne ko ba likita ba harkar lafiya harka ce ta kowa, dukkan mu akwai abinda za mu iya yi, dan haka ina nema da su yada abubuwan da suka samu a yankunansu, yau ne aka fara amma gobe za a iya samun cigaba, dan haka su yada Kuma gobe za mu fara taro a kan koyarwa, akan yadda za a samar da taimakon gaggawa da sauran tarurruka, don haka za mu yi wasu tarurrukan akan aikin lafiya, dan haka ina fatan za su dawo ba ma su kadai ba su zo da wasu su ma su amfana kamar yadda su suka amfana.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Amurka Ta Binne Gawar Al-Baghadadi A Cikin Teku

Next Post

Amfanin Man Zaitun Biyar Ga Lafiyar Jiki

Labarai Masu Nasaba

APC Da PDP

2023: Yayin Da APC Da PDP Suka Yi Jadawali…

by Yusuf Shuaibu
1 month ago
0

...

Buba Marwa

Abin Da Ya Sa Muka Ce A Rika Gwajin Shaye-shaye Kafin Aure – Buba Marwa

by
1 month ago
0

...

Dakta Yusuf Sani

Ba Na Jin Dadin Yadda Ake Yi Wa Malaman Jami’a Kudin Goro — Dakta Yusuf Sani

by Yusuf Sani
2 months ago
0

...

Hodar

Rikita-rikitar Badakalar Hodar Ibilis Ta Su Abba Kyari

by
3 months ago
0

...

Next Post

Amfanin Man Zaitun Biyar Ga Lafiyar Jiki

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: