Daga Abdullahi Muhammad Sheka,
Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da shirinta na sayen manyan motocin sufuri guda 200 da zasu ci gaba da zirga zirga a kwaryar birnin Kano a wani bangare na shirin habaka harkokin sufuri da zai dace da kasaitaccen birni irin na Kano.
Kwamishinan ma’aikatar yada Labarai na Jihar Kano Malam Muhammad Garba ne ya bayyana haka a ranar lahadin data gabata, inda yace, Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bada umarnin hada hannu da kamfanoni masu zaman kansu da hukumar sufuri ta Jihar Kano (KASTA) domin gaggauta sayen manyan motoci 100 domin farawa dasu a kashin farko na shirin kafin karshen wannan shekara.
Yace an tsara daukar wannan mataki ne domin saukaka wahalar da al’umma ke fama da ita na karancin kamfanonin sufuri masu zaman kansu, alokaci guda kuma ayi kokarin magance matsalar matukan babura masu kafa uku dake tukin ganganci, wanda hakan ke neman wuce iyakar hukumomin da ke lura da harkokin cinkoson ababan hawa a Jihar Kano. Malam Muhammad Garba ya nuna cewa yana daga cikin tsare tsaren wannan Gwamnati sake fasalin hukumar sufuri domin biyan bukatun dandazon al’ummar Jihar Kano