Connect with us

TATTALIN ARZIKI

Harkokin Kasuwanci Ya Rasa Tabbas Daga Tattalin Arziki – Rahoton CBN 

Published

on

Harkokin kasuwanci yana cikin matsakaicin yanayi a wannan wata na Yuni, saboda rashin tabbas daga tattalin arziki, wannan bayanin ya zo ne daga cikin saban haroton babban bankin Nijeriya (CBN), wanda ya fitar a makon da ta gabata. Sashen kididdiga na CBN ya bayyana cewa, wannan wata na Yunin shekarar 2020, harkokin kasuwanci ya na bukatar a gudanar da bincike na gabadaya kasar.

Rahoton ya ce, “kamfanoni daga gudanar da harkokin kasuwanci sun bayyana rashin tabbas ga tattalin arzikin kasar nan. Sun dai samu rashin tabbacin ne a harkokin kudade da na an bar bashi da kuma yadda kasuwancin ke gudana dukka yana cikin mawuyacin hali.

“Kamfanonin sun bayyana cewa, su na fuskantar karancin wutar lantarki da gasa a cikin harkokin kasuwanci da hauhawan kudaden haraji da matsalolin kudade da karancin tattalin arziki da rashin samun damar amsar bashi da kuma karancin kayayyakin aiki wanda shi ne babban matsala daga cikin ayyukan harkokin kasuwanci.”

Rahoton ya kara da cewa, kamfanonin sun yi tsammanin darajan naira zai karu a cikin wannan watan, amma suna nan suna saka ido daga watan Yuli zuwa watan Disamba.

“A na tsammanin za a samu hauhawan farashin kayayyaki daga wata shida zuwa wata 12, yayin da za a samu yawan amso basussuka daga wannan watan zuwa wata mai zuwa har dai zuwa wata shida masu kamawa,” in ji rahoton CBN.

CBN ya bayyana cewa, an gudanar da wannan bincike ne a cikin watan Yuni a kasuwanci guda 1,050 daga fadin kasar nan. An samu cimma matsaya a cikin kashi 96, binciken dai ya hada da ayyukan gona da masana’antu masu sarrafawa da masu rarraba kayayyakin da kuma bangaren gine-gine. Rahoton ya kara da cewa, kamfanonin sun kunshi kananan kasuwanci wadanda suke iya sayar da kayayyakinsu a nan cikin gida da kuma kasashen ketare. An tabbatar da cewa, hannun jarin kamfanonin yana raguwa da kashi 24.3 sakamakon matsalolin tattalin arzikin da aka samu a watan Yuni. Ana tsammanin kasuwan hannun jarin kamfanonin zai karu da kashi 31.8 a cikin watan Yuli.

Rahoton ya ci gaba da cewa, ana tsammanin za a samu bunkasar tattalin arziki daga watan Agusta zuwa watan Disambar shekarar 2020, wanda a ke hasashin za a samu karuwar harkokin kasuwanci kashi 47.4 zuwa kashi 67.8 a jamlance.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: