An samu rudani a yankin Ayen da ke karamar hukumar Uhunmwode a jihar Edo lokacin da aka bayar da rahoton cewa wata bindiga da ake kerawa a cikin gida ta tashi kuma harsashinta ya yi awon gaba da marainan wani matashi dan shekara 17 a karshen makon da ya gabata.
An tattaro cewa, yaron mai suna Osaro ya boye bindigar ne a cikin wandonsa kafin ta tashi yayin da yake tafiya.
An kara tattara cewa, harsashi ya yanke marainan ne kuma ya mutu nan take kafin taimako ya zo ma sa.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce, ba wanda ya san yadda bindigar ta tashi, saboda wanda abin shafa ya kasance shi kadai ne lokacin da lamarin ya faru.
Rikicin filayen ya faro ne lokacin da ake zargin al’umman Ayen sun sayar da wasu filaye a yankin na Owegie, kuma matasan Owegie sun hadu zuwa wurin don dawo da kadarorin, kuma a cikin hakan sun yi arangama da samarin yankin na Ayen.
Bayan haka ne ake zargin wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne suka banka wa gidan jama’ar garin Owegie wuta.
Lokacin da aka tuntube shi, kakakin jihar Edo, SP Chidi Nwanbuzor, ya ce, ba shi da masaniya game da lamarin.