CRI Hausa">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Hasashen Masana Kan Alakar Sin Da Najeriya Shekaru 50 Masu Zuwa

by CRI Hausa
February 15, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Hasashen Masana Kan Alakar Sin Da Najeriya Shekaru 50 Masu Zuwa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Masu hikimar magana na cewa, “Juma’a mai kyau tun daga Laraba ake ganeta.” Lallai wannan batu haka yake domin kuwa tun bayan da kasashen Sin da Najeriya suka cika shekaru 50 da kafa huldar diflomasiyya, masu fashin baki ke cigaba da bayyana irin tasu mahangar game da nasarorin da aka samu daga bangarorin biyu a cikin wadannan shekaru da suka shude, musamman bisa lura da yadda alakar dake tsakanin kasashen ke cigaba da karfafuwa, ta fuskokin bunkasar hadin gwiwar cinikayya da tattalin arziki, da al’adu, da makamantansu a tsakanin kasashen biyu hakan ya nuna cewa kwalliya tana biyan kudin sabulu. Sai dai babban fatan da ake dashi bai wuce samun dorewar wannan alaka da cudanya ba har zuwa dubban shekaru masu zuwa. Wannan tunani yayi daidai da sharhin da daraktan cibiyar nazarin al’amurran kasar Sin dake Najeriya, Charles Onunaiju, ya wallafa a wata shahararriyar kafar yada laraban Najeriya ta The National mai taken, “Dabarun cigaban huldar Najeriya da kasar Sin nan da wasu shekaru 50 masu zuwa.” Masanin ya tabbatar da cewa, an samu bunkasuwar hulda cikin sauri a tsakanin kasashen biyu tun bayan da Najeriya da Sin suka kulla huldar diflomasiyya shekaru 50 da suka gabata, kuma yayi amanna cewa kafa ingantaccen salon kyautata alakar dake tsakanin kasashen biyu a shekarar 2005 ya kafa wani muhimmin tarihi game da hadin gwiwar bangarorin biyu. Muddin Najeriya tayi kyakkyawan amfani da wannan damar wajen inganta alakar abokantakar dake tsakaninta kasar Sin, to akwai wasu karin muhimman sakamakon da za a cimma nan da wasu shekaru 50 masu zuwa. Sharhin ya bayyana cewa, hadin gwiwar Najeriya da Sin a fannoni da dama akwai yiwuwar samun manyan sakamako da ake hasashen a nan gaba. Kasar Najeriya tana da muhimman damammaki na albarkatun ‘yan kwadago da kuma saukin farashin kudaden gudanar da ayyuka wanda kasar Sin ke dashi a farkon lokacin kaddamar da manufarta na yin gyare gyare a gida da bude kofa ga waje. Ya kamata Najeriya tayi kyakkyawan amfani da damammakin sauye sauyen tsarin tattalin arziki irin na kasar Sin, da daga matsayin tsarin masana’antunta da karfafa dabarun hadin gwiwa wajen yin musayar tsarin ayyukan masana’antu. Yayin da kasar Sin ta kasance babbar kasuwa da kuma fatan da ake dashi ga tsarin yarjejeniyar cinikayya cikin ‘yanci ta nahiyar Afrika, ya kamata Najeriya tayi kokarin inganta tsarin masana’antunta da karfinta na samar da kayayyaki tare da taimakon kasar Sin, domin zama kasa mafi samar da kayayyaki da fitar dasu zuwa ketare, maimakon zama cibiyar sayan hajoji kawai. A lokaci guda kuma, ya kamata Najeriya tayi koyi da kasar Sin daga irin nasarorin da ta samu wajen yaki da fatara da tsarin shugabanci na gari.(Ahmad Fagam)

SendShareTweetShare
Previous Post

Habasha Ta Yaba Ci Gaban Babban Aikin Meskel Da Sin Ke Gudanarwa

Next Post

Alamomin Ciwon Sanyin Mara Na Maza

RelatedPosts

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

Ci Gaban Kasar Sin A Fannin Fasaha Ba Ya Tsoron Danniyar Amurka

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Daga Bilkisu Xin A ranar 8 ga wata, ma’aikatar kasuwanci...

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

Takunkuman Amurka Da Birtaniya Kan Sin Sun Keta Dokokin Kasa Da Kasa

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon Jakadan Italiya a kasar Sin, Alberto...

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

Masanan Sin Da Afirka Suna Fatan Za A Kara Yin Mu’amalar Al’adu Da Juna

by CRI Hausa
10 hours ago
0

Daga CRI Hausa Kwalajin nazarin harkokin Afirka na kasar Sin,...

Next Post
Sanyin Mara

Alamomin Ciwon Sanyin Mara Na Maza

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version