Hasashen Yadda Za Ta Kaya A Zabukan Shugabannin Manyan Jam’iyyun Nijeriya  

Jam'iyyun

Daga Yusuf Shuaibu,

Shugabanin jam’iyyun siyasa ne suke iya canji yanayin halin da ‘yan Nijeriya suka ciki a yanzu, wajen fatan fitar da dukkanin ‘yan takarar shugaban kasan da ya dace ta hanyar zakulo mutanen da suke da kishi a tsakanin wadanda suka tsaya takarar shugaban kasa. Matukar an samu wannan burin a yanzu, shi ne zai bayar da nasara a zaben shekarar 2023. Domin samun wannan nasarar, dole a magance rikicin da ke tsakanin jam’iyyun siyasar Nijeriya cikin gaggawa domin kauce wa wani sabon lokacin zaben shugabannin jam’iyyun siyasa ko kuma bayan babban zabe.

A cikin kalamun Sakataren Jam’iyyar APC na kasa, Sanata John Akpanudoedehe ya bayyana cewa an amince da ka’idojin da za a gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar a kananan hukumomi da ke fadin kasar nan, wanda kuma su ne za a yi amfani da su wajen zaben shugaban jam’iyyar na kasa. Haka kuma ya sanar da cewa an kaddamar da kwamiti mai mutum uku da za su jagoranci zaban shugaban jam’iyyar na kasa. Sakamakon haka, tsarin salon jam’iyyar a hankali yana ta canzawa wanda zai iya samar da sabon babi a zaben shekarar 2023.

Bin wadannan ka’idoji kan wadanda suke neman kujeran shugabancin jam’iyyar APC na kasa, shi zai kasance wajen tsayar da dan takara kamar yadda jam’iyyr ke kokarin sake zama a kan karagar mulkin kasar nan. Duk wanda ya kasance shugaban jam’iyyar APC na kasa, to dole ne ya shirya tunkarar matsalolin shugabanci da ya gada a wajen shugabannin da suka gabata, domin tabbatar da ci gaban jam’iyyar.

A cikin wadanda suke neman shugabancin jam’iyyar APC sun hada da sanatoci kamar irin su Abdullahi Adamu, Tanko Al-Makura, George Akume, Mohammed Sani Musa and Danjuma Goje. Sauran sun hada da Mallam Mustapha Salihu da tsohon gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff da kuma tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari.

Wadannan jiga-jigan ‘yan takara sun yi wa jam’iyyar hidima ta hanya daya ko ta hanyoyi da yawa. Dukkan ‘yan takarar sun kasance tsofaffin gwamnoni ne banda Sanata Sani Musa da Alhaji Saliu Mustapha. Kasancewarsu tsofaffin gwamnoni, sun bayar da gudummuwa a wasu shekaru wajen jagorantar jihohinsu wanda jam’iyyar ta amfana da su lokacin da suke kan karagar mulki. Sakamakon an samu cin hanci da rashawa da rashin bin ka’ida a lokacin shugabancin tsohon Gwamna Adams Oshiomhole wanda ya shafi mambobin jam’iyyar da kuma shugabannin jam’iyyar. Haka kuama, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince cewa ba zai goyi bayan duk wani tsohon gwamna a zaben shugaban jam’iyyar APC.

A bangare daya kuma, Mallam Saliu Mustapha ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar CPC kuma mamba a jam’iyyar ANPP. Sai dai kuma har zuwa yanzu ba a sami wani dan siyasa daga Jihar Kwara wanda ya nuna sha’awarsa na rike mukami a jam’iyyar APC ba.

A halin yanu dai, Sanata Mohammed Sani Musa dan asalin Jihar Neja yana daya daga ciki masu karfi a tsakanin ‘yan takarar da ke neman shugabancin jam’iyyar APC na kasa, kasancewa ana hasashen za a fitar da shugaban jam’iyyar APC ne daga yankin Arewa ta tsakiya. Sanata Sani Musa wanda yake wakiltar yankin Neja maso Yamma a zauren majalisa ta tara, sannan kuma shi ne shugaban kwamitin gudanar da ayyuka majalisa.

Sai dai kuma jam’iyyar APC ta gaji matsaloli na shugabanci da rikicin siyasa wanda suke bukatar jajirtaccen shugaban kafin ya iya warware dukkanin kalubalen da jam’iyyar take fuskanta.  Bai kamata jam’iyyar APC ta maimaita kuskuren da ta yi a baya ba, domin jam’iyyar tana kokarin samun shawarwari kafin lokacin zaben shugaban jam’iyya. Dole ne masu ruwa da tsaki su bi wasu hanyoyin da suka dace domin magance rikicin jam’iyyar. Bugu da kari, babbar jam’iyyar adawa tana fuskantar irin nata matalolin kamar yadda jam’iyyar APC take fama a halin yanzu.

Ana sa ran samun karin masu tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC na kasa a nan gaba kadan kafin nan da ranar da za a gudanar da zaben jam’iyyar.

Hakadalika, jam’iyyar PDP za ta gudanar da zaben shugabanin jam’iyya na kasa a tsakanin ranakkun 29 zuwa 30 a watan Oktoba. Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP sun amince za a gudanar da zabukan ne bayan wani taro da ya gudana a ranar Jumma’a da ta gabata.
Babbar jam’iyyar adawar ta PDP ta cimma matsaya kan takaddamar shugabancin jam’iyyar na kasa wanda wadansu ke neman sauyin jagorancin Uche Secondus.
Shugaban kugiyar gwamnoni na jam’iyyar PDP kuma  Gwamanan Jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal shi ya fitar da sanarwar zabukan jam kadan bayan kammala taron wanda ya gudana a garin Abuja.

Tambuwal shi ya gabatar da jawabin taron wanda ya bayyana cewa, “Mun gudanar da taro karo na 40 ta wannan babban jam’iyyar PDP tamu, wanda muka samu shawarwarin kwamitin amintattu domin gudanar da zabukan shugabannin jam’iyyar da zai gudana a tsakanin ranar Juma’a, 29 da ranar Asabar, 30 da Lahadi, 31 ga watan Oktoba.

“Mun samu nasarar ganawa da kwamitin amintattu na mutum takwas na wannan jam’iyyar tamu da tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata Dabid Mark, domin shiga cikin tattaunawa na magance rikicin da ke gaban kotu saboda a samu nasarar warware duk wata matsala da ke cikin jam’iyyarmu tare da ci gaba da gudanar da lamura kamar yadda aka saba.

“Ina mai roko a madadin kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ga dukkan ‘ya’yan jam’iyyarmu su hadiye fushinsu domin ciyar da jam’iyyarmu mataki na gaba tare da rungumar zaman lafiya, saboda Nijeriya tana jiran jam’iyyar PDP, na tabbatar muna iya warware duk wata matsala da ke fuskantar jam’iyyarmu.”

Tambuwal ya bayyana cewar matakin gudanar da zaben shi ne hanya kawai mafi sauki da za su bi don samun daidaita masu rikicin da kuma ci gaban jam’iyyar.

 

Rikicin jam’iyyar ya kara kaimi ne bayan da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike da wasu jiga-jigan jam’iyyar suka haso wutar cewar dole sai an cire Uche Secondus daga jagorancin jam’iyyar PDP.

 

Sai dai kuma karar da ke gaban kotu yana barazana da zabukan shugabannin jam’iyyar PDP na watan Oktoba, sakamakon ‘ya’yan jam’iyyar sun ki janye karar da suka kai a gaban kotu.

Duk da dai masu ruwa da tsaki na jam’iyyar da gwamnoni da kwamitin amintattu na jam’iyyar sun zantar da hukuncin, inda majalisar zantarwa na jam’iyyar suka zabi mataimakin shugaban jam’iyyar, Yemi Akinwonmi a matsayin mukaddashin shugaban jam’iyyar, amma shugaban jam’iyyar, Uche Secondus ya dage cewa yana nan kan mukaminsa.

An bayyana cewa magoya bayan shugaban jam’iyyar sun mamaye Babbar Kotun Fatakwal da Korus Ribas domin nuna rashin jin dadinsu ga umurnin da kotunan suka bayar na dakatar da Secondus.

Magoya bayan sun bayyana cewa, “Mun zo kotun ne domin nuna rashin jin dadinmu ga hukuncin kotu, domin mun tabbatar da cewa jam’iyyar PDP tana da tsarin mulkinta. An zabi Secondus ne na tsawan wa’adin shekaru hudu, ya kamata a bari ya kare wa’adin mulkinsa.”

 

Rahotanni daga jam’iyyar PDP sun yi nuni da cewa an sami sabani kan shirin warware rikicin cikin gida tsakanin jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP inda aka yi watsi da wasu matsaya da aka cimma a babban taron kwamitin zartarwata na ranar Talata 10 ga watan Agusta.

 

Haka kuma majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa duk da an amince a taron na ranar 10 ga watan Agusta cewa ya kamata a gudanar da babban taron jam’iyyar a watan Oktoba, kwamitin gudanarwa na jam’iyyar na kasa karkashin jagorancin shugaban jam’iyyar ta PDP Uche Secondus ya gabatar da dalilan da ya sa ba za a iya yin taron a watan Oktoba ba.

 

Sai dai wasu rahotanni daga cikin jam’iyyar sun ce wani bangare a cikin jam’iyyar mai hamayya, wanda ke kakashin jagorancin Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas, ya yi watsi da uzurin Uche Secondus, yana mai cewa dabara ce ta zaunawa daram a matsayin shugaban jam’iyyar ta PDP.

 

Rahotanni dai sun yi nuni da cewa a bisa dalilin sabon rikicin da ke cikin jam’iyyar, akwai yiyuwar a sake yin wani taron kwamitin gudanarwar jam’iyyar wato NEC a watan Satumba.

 

Idan ana iya tunawa a cikin makwanni biyu da suka gabata ne rikicin ya sake barkewa tsakanin mambobin jam’iyyar PDP sakamakon zargin da ake yi wa wani tsagi a cikin jam’iyyar da shirin cire Secondus a matsayin shugaban jam’iyyar.

 

Masu fafutukar na zargin cewa shugaban yana shirin shigar da amintattunsa a matsayin mambobin kwamitin babban taron kasa don tabbatar da sake fitowarsa a matsayin shugaba.

 

A wani bangare kuma, ita ma jam’iyyar APC na fama da rikicin cikin gida tsakanin mambobinta da ake ganin shi ya kawo jinkiri a aikin gudanar da zabubbukan shugabanninta daga matakan gundumomin zuwa sama.

 

Da alama dai wankin hula na neman kai manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya dare, domin kuwa idan suka kasa warware rikicin cikin gida ba za a samu damar zaben shugabannin jam’iyyun da suka dace ba kuma hakan zai shafi fitar da dan takara a kowani mataki. Samun shugabannin jam’iyyar siyasar da suka dace ne ke samar da kyakkyawan dimokaradiyya a ko’ina a fadin duniya. Lallai akwai bukatar wadannan manyan jam’iyyun siyasar Nijeriya su magance rikicin cikin gida kafin su gudanar da zabukan shugabannin jam’iyya.

Exit mobile version