A shekaran jiya ne Allah ya yi wa daya daga cikin ‘yan jaridan da suka yi hidima wa jihar Bauchi, Alhaji Maula Idris wanda ya kammala aikinsa a matsayin babban Daraktan da ke kula da gidajen rediyon al’umma da suke jihar Bauchi (BRC) rasuwa, ya rasu ne a sakamakon rashin lafiyar da ya yi fama da ita.
An yi masa jana’iza da kaisa makwancinsa a jiya Juma’a, inda ‘yan jarida da dama suka nuna kaduwarsu da rashin nasa, kana suna bayyanasa a matsayin mutumin arziki.
A lokacin da wakilinmu ya raka tawagar babban malami a kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin tarayya da ke Bauchi, Hassan Alhaji Hassan kai gaisuwar jaje da ta’aziyya ga iyalan mamacin a gidan marigayin da ke Dutsen Tanshi, babban malamin ya shawarci iyalan marigayin da su rungumi juna da amana.
Ya ce, “Girma ya zo muku, tabbas dukkaninku girma ya zo muku. Wannan hanyar haka take, kowa wa’adinsa yake jira, Allah ya gafarta wa mahaifinku ya sanya aljanna ta kasance masa gida.
Ya shaida wa babban dan marigayin da kaninsa cewa, “ina shawartarku ku kasance masu kula da junaku, dukkanin wani da zai nemi raba kanku kada ku yarda, ku tabbatar da rungumar kannenku da amana ku, kuma jure nauyin girma da Allah ya daura muku,” Inji Hassan Hassa
Kana ya kuma shawarcesu da su ci gaba da runguma ababe masu kyau da mahaifinsu ya rasu ya barsu a kai, ya kuma karfafi ‘ya’yan marigayin dangane da kula da sha’anin iliminsu domin inganta rayuwarsu.
Babban malamin ya yi addu’a ta musamman ga marigayin, yana bayyanasa a matsayin mutumin arziki wanda ya jajirce wajen yin aiki tukuru.