Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Hassan Sani Na Abba: Gwarzonmu Na Mako

by
1 year ago
in DAGA NA GABA
8 min read
Hassan Sani Na Abba: Gwarzonmu Na Mako
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Takaitaccen tarihinka:

Sunan Hassan Sani Naabba, an haife ni a shekarar 1959 kin ga na girmi Nijeriya da shekara 1 kenan. Na yi makarantar firamare a makarantar Shahuci, daga nan na na tafi makarantar Sakandare ta Birnin kudu daga nan na samu gurbin shiga jamiar Bayero ta Kano inada na karanci BSC geography. Bayan na gama wannan karatun na samu aiki a ministry of education aka yi posting ɗina makarantar sakandare ta Bichi. Bayan na yi wata shida ina koyarwa a makarantar sakandire ta Bichi sai na samu wani aikin a ma’aikatar Knupda a Kano a shekarar 1986 har zuwa 2011 ina Knupda sai dai nakan samu canjin aiki na je na kuma dawo shekara 27 na yi ina aikin gwamnatin Kano Alhamdulillahi shekara 18 duk na yi ne a matsayin babban ma’aikaci ina rike da Nigerian position Wanda 1996 zuwa 1999 na yi manajan darakta na Kano state sustainable product a haka dai har ya kai lokacin da na zo na buɗe kamfanina wanda ake kira high standard consultant muna aikin master plan kings wannan aiki ne wanda gwamnati ta ba mu mu yi aikin master plan a Birnin gwari da Ancau A lokacin da nake rike da mukamin manajan darakta a Knupda saia aka buɗe sabon ɓangare a jami’ar Bayero na aikin zayyanar kasa wato (Urban planning) a lokacin ayyuka sun yi min yawa amma kuma ga shi ina son na taimaka musamman da aka faɗa min babu masana da yawa a ɓangaren da za su iya koyarwa don haka na yi alkawari in har na samu sarari zan koyar musamman ma in na yi ritaya. Hakan kuwa aka yi a shekarar 2011 na fara kuma har yanzu ina kai. Kuma ina yinsa ne fisabilillahi ba na neman ko kwabo. Ta haka ne za ka taimaka wa tsarin koyo da koyarwa tunda mu a lokacinmu mun samu kaomai kyauta kuma mai inganci don mai mu ba za mu bayar da gudummawarmu ba?

Sau tari in mutum ya kai wani matsayi musamman a kasar nan sai ka ga ya faɗa siyasa kai ma kana ciki ko ana shiri farawa?
A’a, ni bana siyasa ni ma’aikacin gwamnati ne, kin san yanzu an riga an ɓata siyasar ko ya aka ce ka je manajan darakta to shikenan sai alakantaka da siyasa. Amma tun daga lokacin da malam Ibrahim Shekarau ya jawo ni na yi manajan darakta a gaskiya a duk wani abu nashi na siyasa idan ya taso gaskiya muna fitowa kwanmu da kwarkwatarmu duk yanda za mu taimaka mu taimaka domin ɗan halas ke mayar da biki malam ya rikemu hannu bibbiyu ya yi mana shugabanci na gari sai dai mu ce masa Allah ya saka masa da alheri Allah yasa ya gama lafiya.

Labarai Masu Nasaba

Ibrahim Gurso (1794-1814)

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Nasiru Muhammad (2)

To, amma ya ka ke kallon Siyasa a Yau tunda kana shiga alamuransu?
Siyasa abu ce mai kyau tunda dai tsarin tafiyar da mulkin alumma ce ta hannun alummar amma inda matsalar take mu a wurinmu mai makon mu mayar da hankali kan ci gabanmu ta kan alheran da siyasar ta kawo sai muka ɓige da ganin laifin juna da da zargin juna. Yanzu misali a Kano kana kallon abubuwa ana yi ba dai-dai ba amma kana tofa albarkacin bakinka sai a siyasantar da maganar amma a ko’ina a duniya inda ake siyasa duk cigaban da ake samu wurin da ake shugabanta ne suke samu don al’ummar ce a gabansu amma mu anan da dama mutanenmu na shiga siyasa ne don ci gaban kansu.

Wanne abu ne ba za ka taɓa mantawa ba a gwagwarmayarka ta aiki?
To kin san yanayi ko rayuwar aiki tana tafiya ne da rayuwarka don haka abubuwan suna da yawa amma muhimmai da har yanzu in na tuna ina jin daɗi ko ina mamakin wai ni na yi ? ba su da yawa misali a ciki akwai
Lokacin ina MD Housing a lokacin ma;aikatar ta tsaya cik gwamnati ba ta da kuɗin gina gidajen sannan ba ma ta da kuɗin ko da biyan albashin ma’aikatan kuma duk nauyin na kaina don haka na rasa yadda zan yi komai ya yi min zafi ga shi ni burina na kawo sabon abu wanda zai kawo ci gaba wannan ɗabi’ata ce in na gan ni a wuri don haka na rasa inda zan sa kaina ba na son gazawa don haka na shiga laluben mafita. Don haka na kira daraktocina na shaida musu tunda muna da filaye kawai mu sanar a gidajen radiyo za mu fara gina gidaje kuma duk mai so ya ajiye dubu ɗri biyar. Nan da nan sai ga mutane da yawa sun fito sun ajiye kuɗadensu a lokacin muka samu kusan miliyan hamsin. Da wannan kuɗin muka yi DVC na gidaje guda hamsin. Don haka muna kammalawa muka kuma yin shelar wanda yake bukatar gida da gaggawa ya kawo kuɗi nan da nan sai ga an kammala gidaje na Zawaciki har da rara na biyan albashi. Haka yake a ɓangaren masu kashe-kashen kaya a bakin titi su ma don a lokacin kasuwanci ya dawo kan titi don haka kowa na karya doka yadda ya ga dama ganin abun ya lalace a lokacin ma ba na Knubda amma sai aka ce a dawo da ni ni zan iya kawo karshen abun. Bayan na dawo sai na fara tunanin yadda zan tashi mutane.
Don haka na shiga laluben hanyoyin da zan bi don kawo gyara amma ba tare da na kuma cusgunawa masu neman abinci ba a wajen. Duk das u ma masu kasa kayan a kan titin ba a kan dai-dai suke ba an yi titi ne don a wuce mai abin hawa ko mai tafiya a kasa amma sai mai gawayi ko mai tumatir ya kasa mai tattasai ko mai kosai da sauransu. Don haka dole a samu doka ba za mu bari abin ya lalace ba. Matsalar su ma’aikatan ba su tunanin cewar amana aka ba mu don haka sai ake saka son zuciya a cikin al’amuran.
Lokacin da muka muka gama planning din abin da ya dace sai muka je muka kai wa coucil bayan mun kai sai malam Shekarau ya ce ya yarda da abin da muka rubuta amma da sharaɗi guda na duk wanda muka tasa to sai mun kai shii sabon matsugunni inda zai ci gaba da sanaarsa. Amma saboda rashin amanar da ke tsakanin talakawa da gwamnati a baya sai mutanen nan suka sa shakka amma daga baya da su ka ga wasu sun samu rumfuna sun tashi sai gasu har suna kuka.

Me ne ba za ka taɓa mantawa ba a aikin da ka yi?
Wato abubuwan suna da yawa amma abun da na rike darasi shi ne ɗan’adam ba ka iya masa. Duk da abubuwan da malam Ibrahim Shekarau ya yi na alheri a lokacin na ba wa duk wanda aka tasa matsugunni amma sai da ‘yan adawa suka ga an yi ba dai-dai ba suka ci gaba da azababbiyar adawa. Ba na mantawa Kan hanyar BUK mun zo muna tashin mutane alokacin an taso yan sakandare sai suka rika zuga yaran suka rinka jifanmu aka jefeni a fuska har sai da fuskata ta kumbura hakora na duk suka kumbura. Ganin yadda aka yi min ya sa lallai ma sai wannan programe ɗin ba fashi.
To, alhamdulillahi wannan lokacin n wannan mun tayar da mutane wurin dubu takwas, mun kuma samar da kasuwanni kusan guda takwas manya- manyan. Kasuwannin sun haɗa da GSM billage na farm center mu muka yi ta tana ɗaya daga ciki akwai kasuwa a Bachirawa akwai kasuwa a Rijiyar Zaki duk wadannan a lokacin mu muka kirkireta domin mu tsugunar da mutane kuma mu kai wannan aka tsugunar da mutane. Tun daga BUK road har zuwa wajen gidan Murtala duk muka tayar da mutane mu kai gyara shi muka daddasa bishiyoyi domin a gyara gari a kawo yanayi mai kyau.

Waɗannan Rumfunar Kyauta ne ko haya ku ka bayar da su?
Kyauta ne ba ma bukatar ko sisi muke Basu wani tsari mukai kamar yadda nake faɗa miki ni kullum tsari na da tunanina in kawo wani abu sabo don haka muka na yi tunanin wanne tsari za mu yi. Don haka sai muka fara neman filaye manya-manya a irin haka muka yi ta samun filayen sannan kuma muna haɗaka za mu ba wa mutane su gina kasuwanni duk shekara za su ba ka dubu goma a dubun goman nan kai za ka ɗauki dubi bakwai gwamnati za ta ɗauki dubu uku. A lissafinmu na wancan lokacin a filin da muka yi kasuwa a Bachirawa zai karɓi miliyan Ishirin da ɗaya idan muka karɓa mai fili zai amshi miliyan goma sha huɗu gwamnati za ta rike miliyan bakwai. Ba na mantawa a lokacin da na aika ma mai filin Bachirawa da sako na cakin kuɗi na wannan filin sai ga mai filin ya zo ya same ni a ofis ya ce min “MD wannan wurin kwace min ku ka yi ko kuma siya ku ka yi?” Na ce a’a wannan yarjejeniya ce da muka yi da kai kamar yadda na gaya ma shekara goma in shekara goman ta cika wurin nan zai dawo gunka gaba ki ɗaya. Kuɗin Nan da muke karɓa kai ne za ka dinga karba, kasuwa ta zama taka gaba ki ɗaya. Yin haka an taimakawa mutane sun sami aikin y,i shi kuma mai guri an taimaka masa.

Ya ka ke ganin cigaban Kano a yanzu ta hanyar kasuwanci da zamantakewa?
Kin ga Kano dole a yi tsari ya zama cewar yadda take cibiyar kasuwanci din nan da ake faɗa kuma dole ne a samu mafita da yanayin halin da ake ciki. Talaucin nan da ake ciki da kuma lalacewar abubuwa dole ne a samu mafita. Babbar matsalar mu kamar yadda na faɗa shi ne rashin shugabannin da za su tsaya su fitar da gaskiyar magana a tsaya a bi ta. Amma sai ki ga da yawa daga cikin shugabannin da ake zaɓe kowa zai hau mulki sai ki gad a wani abu a zuciyarsa. Ba na mantawa mun taɓa zuwa wurin marigayi sarkin Kano mu uku kan irin wannan damuwar ta yadda za a zamana akwai shugabanci da tsari a jaha.

Da akwai wani abu guda na Duk wanda ya tarar da aiki ba zai ɗora akai ba sai dai ya kirkiri sabo?
Shi ma dai batun tsari ne kawai ne duk da dai yanzu akwai links misali akwai na su Shatu Ɗankani da Alhaji Bashir Tofa kuma duk suna ta tsare-tsare na ɗorewar ayyuka da tsari na duk wanda ya zo gwamnati ba zai je ya yi abin da yake so ba dole ya bi tsari. Misali lokacin mulkinmu mun faɗaɗa titin gidan gwamna da na Ibrahim taiwo da na gidan Zoo, akwai biyu a sabon gari da Bank road su duk mu muka mai da su hannu biyu zuwa uku. Amma sai ki ga in wata gwamnati ta taho sai ki ga ba lallai ne ba ya ɗora akan aikin da ya gada. Ya kamata duk gwamnatin da ta zo a nuna mata inda aka tsaya

Me ka ke gani matsalar matasa a yau?
Babbar matsalar matasanmu a yau shi ne raina sana’a. Za ki ga mutum ya taso daga makwabtan jihohinmu kamar Zamfara ko Katsina ya zo Kano za ki ga suna sana’arsu komai kankantarta ba sa raina sana’a amma mu namu yaran sai ki ga sun raina. Sannan kuma gwamnati ya kamata ta nemawa yaranmu abin yi. Misali a lokacin muna gwamnati sai muka yi tsari yaran a saita su ayi musu tsari a nuna musu rayuwar ga yadda take. A lokacin muka buɗe katon wuri wanda za a ringa gyaran wayoyi muka kira kamfunan Chana suka zo suka dinga koyawa yaranmu yanda za a gyara wayoyin, da ma yanda za a yi wayar ita kanta. To ire-iren wannan damar ya kamata a ba wa matasa don su dogara da kansu. Sannan su ma matasan su rage lalaci da jin kai su rungumi sana’a ba kullum suke hangen aikin gwamnati ba. Amma duk da haka yanzu yadda abubuwa suke nunawa akwai gyararraki za su zo ba da jimawa ba insha Allahu. Ita fa Kano kamar New York ce ko Amirka Kano garin baki ce don haka cibiya ce da ya kamata a ce kullum ana ganin ci gaba a cikinta. Sannan ya kamata a farfaɗo da masana’antu wanda yin hakan zai taimakawa ‘yan kasuwa da kasuwanci da samar da ayyukan yi ga matasanmu.

Wane fata gare ka ga Kanawa?
Fatana ga Kanawa shine Allah ya kuma zaunar da jiharmu lafiya ya ba mu tsaro ya da kwanciyar hankali. Allah ya kara taimake mu Kano ta zama garin da kowa yake sha’awa da kuma cigaba mai yawa Insha Allahu. Allah ya yi wa garin albarka da ma kasa baki ɗaya. Allah ya yi wa shugabanninmu jagora, amin.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Sheikh Dahiru Bauchi: Ba Wanda Ya Kai Buhari Son Nijeriya

Next Post

Kungiyar Likitoci Na Shirin Tsunduma Cikin Yajin Aiki Ranar Alhamis

Labarai Masu Nasaba

Ibrahim Gurso (1794-1814)

Ibrahim Gurso (1794-1814)

by
12 months ago
0

...

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Nasiru Muhammad (2)

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Nasiru Muhammad (2)

by
1 year ago
0

...

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Umaru Ibrahim Battaiya

Gwarzonmu Na Mako: Alhaji Umaru Ibrahim Battaiya

by
1 year ago
0

...

Ladan

Marigayi Alhaji Yusuf Ladan: Gwarzonmu Na Mako

by
2 years ago
0

...

Next Post
Kungiyar Likitoci Na Shirin Tsunduma Cikin Yajin Aiki Ranar Alhamis

Kungiyar Likitoci Na Shirin Tsunduma Cikin Yajin Aiki Ranar Alhamis

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: