Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi
Rahotanin dake fito wa daga garin Yauri a jihar Kebbi kan yawan hatsarin jiragen ruwa da ambaliyar ruwa da aka yawaita samu a cikin wata ɗaya, wadda yakai kimanin hatsarin jirgin ruwa uku zuwa huɗu a wata ɗaya a masarautar Yauri a jihar ta Kebbi.
Jama’a da dama a yankin na masarautar ta Yauri a Kebbi na ganin cewa hukumomin gwamnatin da abin ya shafa suna yi wa lamarin riƙon sakainiyar kashi kan haɗuran da ake yawan samu a jihar, domin yankin na Yauri da ma jihar bakin ɗaya na cikin jimamin asarar rayuka da dukiyoyi.
Hat yanzu dai maganar ake yi cewa mutun nawa ne suka rasa rayukansu, babu wata takardar da ke nuna cewa ga iya adadin mutanen da jirgin ruwa ya ɗauka, domin kowane mutun ya zo bakin tashar ta jiragen ruwa zai shiga ne kawai, idon aka ga jirgin ya ɗauki mutanen masu yawan gaske kuma ga kayan su, sannan jiragen ruwa ke tashi zuwa ƙauyukan da za su je.
Haɗarin dai shi ne na uku dake ya auku a garin na Yauri a jihar ta Kebbi , inda iyalan na gidan Alhaji Abdullahi Maikano Rukubalo sun fito ne daga gonarsu da suke aikin noman albasa a wani ƙauye da ake kira Hikiya a cikin ƙaramar hukumar mulki ta Yauri kan hanyarsu ta zuwa ƙauyen su a ranar Alhamis ta makon da ya gabata, da misalin karfe shida na yamma, sai iska hadari ya taso kuma lokacin suna cikin kogin ruwan da nufin zuwa gida, sai igiyar ruwa da yake kaɗawa da ƙarfi sosai, ga shi kuma ruwan sama ya sauko shi ne sai jirgin ruwa nasu ya kaɗa jirgin ya nutse cikin ruwa.
Wakilin LEADERSHIP A Yau dake Birnin-Kebbi ya samu zantawa da yaran da Allah ya tsirar da rayuwar su a hatsarin jirgin ruwa kwale-kwalen a yankin na garin Yauri, inda Yahuza Abdullahi da Babangida Abdullahi suka ce, “Alhamdullah daAllah ya kare rayuwarmu a cikin hatsarin jirgin ruwan kwale-kwale da ya rusta da ‘yan gidanmu lokacin da muke fito wa daga gona wurin aikin noman albasa a garin Hikiya, bayan mun tashi gona zuwa gida a Rukubalo. Bayan mun shiga jirgin sai muka ga iska da kuma ruwan sama, sai kawai igiyar ruwa ta taɗawa jirginmu, daga nan mu duka muka nutse cikin ruwa kogin.”
Haka zalika sun ci gaba da cewa, “daga nan bayan an fitar da mu cikin ruwan kogin, saboda haka bayan wannan bayanin bamu iya bada sauran labarin abin da ya faru ba.
Shi ma wani na kusa da iyalan Alhaji Abdullahi Maikano Rukubalo Baban magariyan da kuma yara biyu da suka tsara da rayuwarsu ga hatsarin jirgin kwale-kwalen ya samu zantawa da LEADERSHIP A Yau mai suna Malam Nasiru Gungun Sarki ya ce, “kawo yanzu babu wani tallafi da aka kawo ta hannun gwamnatin amma Sarkin Yauri ya bada tallafin kuɗi ga iyalan na Alhaji Abdullahi Maikano Rukubalo da ya rasa yaran a makon da ya gabata”.
Har ila yau wani ɗan uwa ga iyalan Alhaji Abdullahi Maikano Rukubalo mai suna Suleiman Umar Rukubalo shi ma ya ce “har yanzu banmu samu wani tallafi daga gwamnatin ba ko wasu hukumomin da abin ya shafa. Amma Sarkin Yauri ya aiko tallafin kuɗi ga iyalan.”
Domin jin ɓangaren gwamnati, LEADERSHIP A Yau ta samu jin ta bakin Sanata mai wakilta yankin da wannan lamarin ya auku, watau Sanata Bala Ibn Na’Allah inda ya ce, a ranar 5 ga watan nan ya gabatar da takardar koke a gaban majalisar dattawa kan kira ga gwamnatin tarayya da kuma hukumomin da abin ya shafa domin bada tasu gudunmuwar da kuma shigo wa ciki domin magance matsalar hatsarin jiragen ruwa da ake yawan samu kai har ma da matsalar ambaliyar ruwa a yankuna jihar ta Kebbi. Wanda mataimakin Shugaban majalisar dattawa Sanata Ikweremadu ya jagoraci zaman a lokacin da ya gabatar da koken na mutanen yankinsa.
Sanata ya ce, ya zama wajibi gareshi a matsayin Sanata mai wakiltar mutanen mazaɓar Kebbi ta Kudu ya tabbatar da cewa an magance wannan matsalar. Haka zalika ya ce yawan hatsarin jirgin ruwa da ake samu a jihar ta Kebbi ya zama abin tashin hankalin mutanen yankinsa a jihar Kebbi, saboda haka ya ce kamar yadda ya faɗa tun farko cewa ya zama wajibi gareshi ya yi kira ga gwamnatin tarayya da kuma duk hukumomin da abin ya shafa .
Sanata Bala Ibn Na’Allah ya ce, “a halin yanzu ya tuntuɓi mataimakin shugaban ƙasa Farfesa Yemi Osinbajo domin yin ƙoƙarinsa na ganin an magance matsalolin hatsarin jirgin ruwan da ake yawan samu a cikin kogin Neja da ke da iyaka da wasu garuruwan na yankin Kebbi ta Kudu, inda yake wakilta a majalisar dattawa”.
“Na haɗu da mataimakin shugaban ƙasa, domin neman biyan buƙatur mutanen da nake wakilta ga gwamnatin tarayya kan wannan matsalolin da suka Faru. Ina tsammanin samun taimakon daga gwamnatin tarayya nan ba da jimawa ba”. In ji shi.