Rukayyat Sadauki">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MATASAN ZAMANI

Hatsarin Karuwanci A Manyan Makarantu

by Rukayyat Sadauki
January 29, 2021
in MATASAN ZAMANI
3 min read
Hatsarin Karuwanci A Manyan Makarantu
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Cigaba da yawaitar karuwanci a cikin manyan makarantun gaba da sakandire a Nijeriya, babbar matsala ce da ta ke bukatar ‘Yan Nijeriya gabadaya su farka daga barci su maida hankali a kai su yi duk abin da ya dace domin magance wannan matsala. Masu iya magana sun ce “matasa su ne shugabannin gobe”, su ne za su jagoranci al’umma su kuma tsara wa jama’a manufofi da tsare-tsare a rayuwa tagaba. Saboda haka idan ya kasance matasa suna fadawa cikin harkar karuwanci da miyagun dabi’u, to shakka babu kasa ta na cikin hatsari mai girma.

Saboda makudan kudaden da ake samu a wannan haramtacciyar sana’a, wadannan rukuni na karuwai a manyan makarantun gaba da sakandire kan samu kaya na alfarma da abubuwan bajinta daga abokan huldarsu domin nuna bajinta da kece raini a tsakanin abokan karatunsu. Idan ka ziyarci wuraren kwanan dalibai mata (Hostels) a manyan makarantun gaba da sakandare da daddare, abu na farko da zai fara baka mamaki shi ne manyan motoci na alfarma da za ka gani wadanda suka zo domin su dauki ‘ƴan mata dalibai su tafi wuraren casu ko fati da sauran yawon shakatawa da su. Hatta dalibai mata a yanzu sun kasance dillalan mata ga masu dukiya su na biyansu su samar musu da wadatattun ‘ƴan mata dalibai.
Ta’azzarar matsalar karuwanci a tsakanin ‘ƴan mata dalibai, abin damuwa ne matuka sannan kuma gagarumar matsala ce wacce ta ke neman ta zarce sauran matsalolin da ake fama da su a cikin al’umma, kamar matsalar kungiyoyin asiri da matsalar fashi da makami da matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi da ke addabar manyan makarantun kasa.
Wannan burin samun dukiya ta haramtacciyar hanya da kuma fidda tsammani daga mafi yawan ‘Yan Nijeriya musamman ma wadannan ‘ƴan mata da ke karatu a manyan makarantun gaba da sakandire, abubuwa ne da su ke sanya su fadawa aikata fasadi da zinace-zinace ba tare da tunanin kamuwa da cuta mai karya garkuwar jiki “kanjamau”, (HIb/AIDS) da sauran miyagun cututtuka masu kisa da ake kwasa ta hanyar jima’i ba.
Rashin tarbiyya a makarantu matsala ce da ke jagorantar tabarbarewar al’amura a manyan makarantun gaba da sakandire, a mafi yawan lokuta Jami’o’i kan ba da kariya ga masu dukiya da suke aikata fasadi da ‘ƴan mata dalibai ta hanyar girmama su da lambobin yabo na digirin girmama da kuma daure musu gindin cigaba da lalata da ‘ƴan mata. Muna cikin hatsari mai girma a wannan kasa matukar ba mu tunkari wannan matsala da gaske mun murkushe ta ba. Amma tambayar ita ce; wa ke samar da dandalin cigaba da gudanar da wannan, a lokaci guda zai iya ya kasance ‘ƴan siyasa, masu rike da madafun iko da attajirai na daga cikin manyan masu taimaka wa cigaba da bunkasar wannan mummunar sana’a a muhalli na farko.

Wadanna su ne ya kamata a ce sun kasance ginshikan masu tarbiyyar gina al’umma, sai dai a yanzu sun zamto masu rusawa. Saboda haka ya zama wajibi ga iyaye su sanya ido sosai a kan ‘ƴa’ƴansu tare da ba su kykkyawar tarbiyyar da za ta haska musu hanyar da za ta jagorance su ko da ba sa a tare da su.
Masana halayyar dan adam sun tabbatar da cewa cigaba da dorewar matsalar karuwanci a manyan makarantun gaba da sakandire, matsala ce da za ta taba nagarta da darajar matasa masu tasowa wadanda za su kasance shugabannin kasa a rayuwa tagaba. Haka zalika matasa ‘ƴan mata masu tasowa su na daukan kaso mai yawa na adadin jama’ar kasa. Cigaba kadan za mu tsammata daga gare su idan ya kasance su na fadawa cikin zinace-zinace da fasadi.
Sannan daga Allah ne; babu wani abu da ke sanya kokwanto ga iyaye kan halayyar ‘ƴa’ƴansu musamman ma idan aka zo batun kamewa daga aikata zina. Idan ya kasance yarinya an hore ta kan jin tsoron Allah da girmama sauran mutane da kuma kallo jikinta a matsayin ayar Allah ba za ta samu rudu da matsin lamba ba.
Duk yadda za a yi, ya zama wajibi a gudanar da bincike a cikin birane a gano manyan makarantun da ake aikata wannan harka ta karuwanci. Domin karuwanci a manyan makarantun gaba da sakandare a yanzu ya wuce yadda ya ke ada, a yanzu karuwanci ya zama kasuwanci na zamani da ake gudanar da shi cikin tsari, kuma ba wai iya yara mata dalibai ne kawai su ke yi ba har ma da yara maza ana saduwa da su kamar mata domin samun abin duniya.
Babu wata kasa da za ta tsira ko ta samu wani gagarumin cigaba idan ya kasance matasanta masu tasowa wadanda ake da yakinin su ne shugabannin gobe ba su da kyawawan halaye da dabi’a masu kyau. Babu wani abu da za su iya amfanawa kasa da al’umma saboda munanan dabi’unsu sun rusa martaba da kima da darajar al’umma ta hanyar karya ginshikin da ya hada su da jama’a. Har wa yau mu na cike da fata da addu’ar yin bankwana da wadannan matsaloli a manyan makarantunmu tare da fatan ganin an gina tushen al’umma mai nagarta da kyawawan halaye da dabi’u.

SendShareTweetShare
Previous Post

Tarihin Kabilar Ewe Da Abubuwan Da Suka Gada Na Gargajiya (III)

Next Post

“Duk Da An Sauya Shugabannin Tsaro, Har Yanzu Da Saura”

RelatedPosts

‘Yar Shekara 28 Ta Bude Wujen Koyar Da Sana’o’in Mata A Kano  

by Rukayyat Sadauki
1 month ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, Wata budurwa mai shekaru 28 a...

Matasan Nijeriya Mu Farka Matukar Muna Son Ganin Cigaban Kasa

Matasan Nijeriya Mu Farka Matukar Muna Son Ganin Cigaban Kasa

by Rukayyat Sadauki
8 months ago
0

Daga Ibrahim M. Nasir Masu iya magana sun ce “matasa...

Tasirin Hanyar Sadarwa Mara Tsari Wajen Yada Labaran karya

Tasirin Hanyar Sadarwa Mara Tsari Wajen Yada Labaran karya

by Rukayyat Sadauki
9 months ago
0

-Sadarwa Marar Tsari, Ta Na Kasancewa A Gidaje Da kungiyoyi...

Next Post
“Duk Da An Sauya Shugabannin Tsaro, Har Yanzu Da Saura”

“Duk Da An Sauya Shugabannin Tsaro, Har Yanzu Da Saura”

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version