Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 23 Da Jikkata 33 A Neja

by Muhammad
December 30, 2020
in LABARAI
1 min read
Hatsarin Mota
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Khalid Idris Doya,

A kalla mutum ashirin da uku (23) ne aka tabbatar da mutuwarsu yayin da wasu karin mutum 33 suka gamu da munanan raunuka sakamakon hatsarin motar Tirela a kauyen Masha da ke kan hanyar Makere-Mokwa a jihar Neja da yammacin ranar Litinin.

Har-ila-yau, Shanu da Awaki da dama ne suka hallaka sakamakon wannan hatsarin.

Babbar motar wacce ta kwaso shanu da wasu kayayyakin gona tare da mutane a cikinta da niyyar zuwa kudancin kasar nan kila domin gudanar da harkokin kasuwanci.

Mutum sama da 55 ne aka bada rahoton cewa su na cikin babbar motar lokacin da hatsarin ya faru, sai dai direban motar da Karen motarsa babu abun da ya samesu kamar yadda ganau suka shaida.

An kwashi dukkanin wadanda suka jikkatan zuwa babban asibitin Mokwa domin nema musu jinya daga wajen kwararru wanda yanzu haka su na kan amsar kulawar jami’an lafiya, inda kuma aka kwashi wasu daga cikin gawarwakin zuwa dakin adana gawarwaki na asibitin.

Shugaban shiyya na hukumar kiyaye hadura ta kasa (FRSC) a jihar ta Neja, Mista Joel Dagwa, ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar manema labarai da ya fitar, inda yake mai cewa hatsarin ya rutsa ne da wata babban mota Daf Trailer (kirar 95).

Dagwa dai bai bada lambar motar da ta samu hatsarin ba, sai dai ya gargadi direbobi kan tsula gudun tsiya a kan hanya.

Shugaban ya bayyana cewa motar ta taso ne daga jihar Kebbi wacce ta nufi jihar Legas, “Dukkanin mutanen da suke cikin tireban maza ne,” inji shi.

SendShareTweetShare
Previous Post

Matasa Miliyan Biyu Suka Rasa Aiki Sakamakon Dakatar Da Rijistar Layin Waya

Next Post

Marigayi Maji Dadin Kano Mutum Ne Mai Kaunar ’Yan Kasuwa – Ketawa

RelatedPosts

Jami’an NIS Na Samun Horo A Kan Amfani Da Dokokin Shige Da Ficen ƙasa

Jami’an NIS Na Samun Horo A Kan Amfani Da Dokokin Shige Da Ficen ƙasa

by Sulaiman Ibrahim
6 hours ago
0

Shirin yaƙi da safarar bil’adama da fasa-ƙwaurin ‘yan gudun hijira...

‘Yan Nijeriya Mutum Miliyan 15 Na Shan Kwayoyi, Inji Buba Marwa

‘Yan Nijeriya Mutum Miliyan 15 Na Shan Kwayoyi, Inji Buba Marwa

by Muhammad
9 hours ago
0

Shugaban Hukumar NDLEA mai yaki da sha da fataucin miyagun...

Katin Zama Dan Kasa

Nijeriya Ta Wajabta Wa Jami’an Diflomasiyya Mallakar NIN

by Sulaiman Ibrahim
15 hours ago
0

A jiya Lahadi Gwamnatin Tarayya ta shaida cewar, ya zama...

Next Post
Maji Dadin

Marigayi Maji Dadin Kano Mutum Ne Mai Kaunar ’Yan Kasuwa – Ketawa

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version