Hatsarin Mota Ya Ci Rayuwar Dalibin ATAP Mai Shirin Tafiya NYSC

Dalibin

Daga Khalid Idris Doya,

Wani dalibin da ya kammala karatunsa da ke zaman jiran tafiya hidimta wa kasa wato (NYSC) nan da wata daya kuma mai fama da lalura ta musamman (Nakasa), Malam Muhammad Buhari Jamda ya rigamu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ta rutsa da shi a Bauchi.

Marigayi, wanda ke fama da kasa wanda ya kammala karatun darasin koyon aikin jarida matakin babbar Diploma (HND) a kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin jihar Bauchi, ya rasu ne a ranar Litinin biyo bayan raunuka da ya gamu da su sakamakon hatsarin da ta riske shi a ranar Asabar.

Mun nakalto cewa matashi mai neman cimma burinsa a rayuwa Jamda, kafin rasuwarsa shine sakataren hukumar kula da nakasassu ta jihar Bauchi.

Magayin wanda suka yi taho mu kara da mai mota a yayin da shi kuma ke kan Babur din masu fama da nakasa lamarin da ya kaisa ga dungulawa da hantsilawa da har hakan yayi ajalinsa.

Daya daga cikin manyan malaman tsangayar koyar da aikin jarida na kwalejin kuma tsohon ko’odinetan shirye-shirye, Malam Abdul Burra, ya misalta wannan rashin a matsayin babban rashi mai sosa zukata da suka ji zafinsa matuka.

Malamin a sakon da ya wallafa ya shafinsa a ranar Talatar nan da ta gabata na cewa, “Cike muke da alhini da jimami gami da kaduwar sanar da rasuwar Malam Muhammad Buhari Jamda sakamakon hatsarin da ta sameshi a kan hanyar Bauchi Club.”

Ya nuna cewa, Buhari ya kasance wani matashi mai kokarin tabbatar cimma muradinsa da manufofinsa na rayuwa duk da kasancewarsa mai fama da nakasa bai kashe zuciyarsa ba, inda ya nufi rayuwa bisa matakan da suka dace da har ya sanya shi ke sha’awar zaman dan jarida.

Ya ce: “Shi din dalibina ne mai matakin karatun babban diploma mai daraja (HND) wanda daga baya ya maidani matsayin uban gidansa. Kowani rana yana zuwa ofishina domin ya gaidani ya ganni domin neman shawarori kan lamuran da suka shige masa dubu.”

Ya sanar da cewa, duk da marigayin gurgu ne, amma ya kasance mai kwazo, hazaka da fikira a cikin aji.

A cewarsa, marigayin yana mutunta dukkanin ababen da suka tabbatar za su kaisa ga cimma muradinsa da burinsa na rayuwa a tare da duba wahalar lamarin ba.

“Makonni kalilan da suka wuce, ya gaya min cewa suna shirye-shiryen tafiya hidimta wa kasa (NYSC) ya nuna cewa suna fatan za su tafi sansanin hidimta wa kasa a wata mai zuwa, bai ma sani ba, kan cewar rayuwarsa ba za ta kaisa zuwa ganin wannan hidimta wa kasar ba,” inji malamin nasa.

Daga nan, Malam Burra yayi addu’ar Allah ya jikan mamacin ya sanya aljanna ta zama masa gida na karshe a rayuwarsa, kana ya nemi sauran masu irin lalura tasa da su yi koyi da marigayin wajen tsayuwa kyam domin neman cimma muradinsu na rayuwa.

Exit mobile version