A kalla mutane 20 ne suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon hadarin mota da ya faru a karamar hukumar Tureta da ke Jihar Sokoto.
A cewar shaidun ido, lamarin ya faru ne a kauyen Bimasa misalin karfe 6 na yamma a ranar Alhamis a yayin da mota kirar Gulf ta yi karo da wata Toyota Hiace dauke da fasinjoji
Abin babu dadin kallo. Mun kirga a kalla fasinjoji 20 da suka mutu a nan take yayinda wasu da dama sun samu munanan raunuka,” a cewar wani mazaunin kauyen da ya ziyarci inda abin ya faru.
Kakakin ‘yan sandan Jihar Sokoto, Sadiq Abubakar a jiya ya ce sun tabbatar da mutuwar mutum 19, inda ya kara da cewa wasu mutum 14 da suka jikkata sakamakon hatsarin suna samun kulawa a asibitin koyarwa na Jami’ar Danfodio, UDUTH, da ke Sokoto.
Wani shaidan ganin ido, Malam Nura, ya ce idan ba don gudun da direban Gulf din ya ke yi ba da hatsarin bai faru ba.
“Kaga akwai rami sosai a titin amma duk da hakan direbobin Gulf da Sharon na haya sukan rika zura gudu tamkar za su tafi lahira,” in ji shi.