Dakta Aliyu Ibrahim Kankara" />

Hattara Dai Matan Katsina!

Daidai gwargwadon hali na yi yawo a wannan sarari na Subhana. A nan gida Katsina, na yi yawo tun daga Dankama har Damari, na shiga lunguna-lunguna, sako-sako. A cikin kasar nan, na yi zirga-zirga, na yi yawo kwararo-kwararo: tun daga inda Kanuri su ka fi yin sansani har zuwa bakin teku (Ikko garin Turawa); tun daga Birnin Shehu har Eket inda ake tsiba kasuwar karnuka kumbi-kumbi kamar kara inda ake sayar da awaki ko tumaki a nan gida Arewa. A wajen kasar nan, na zagaya wasu daga cikin kasashen Karamar Nahiyar Asiya. A Afirka, na shiga kasar Nijar lungunan ta da kwararon ta kamar yanda mutum za ya shiga dakin sa. Na sadu da jama’a iri-iri masu al’adu da addinai iri-iri, wasu masu ban sha’awa wasu masu ban takaici, wasu masu ban haushi, wasu kuma ga su nan dai, kadaran-kadahan. A wani wurin, za ka tarar da wasu al’ummomin ga su dai musulmai amma ba su kaunar ka, kai musulmi sabili da ba irin launin fatar ku daya ba. Amma duk inda na yi yawo din nan da saduwa da mutane ban taba cin karo da mutum mai son jama’a mai son yin tarayya da mutane mai kuma saukin hali da sanin-ya-kamata, fasihi, mai addini mai tsari mai kyau, mai hankali, mai halaye nagari abin koyi, abin sha’awa kamar Bahaushe ba.

Saboda al’adun sa da tabi’o’in sa da irin yanayin dangantakar sa da sauran mutane, da iya shiga-da-fita na kasuwanci da tsare amana Bahaushe ya ke mafifici abin sha’awa ga kowanne irin jinsin mutum. A Duniya, Bahaushe ne kadai aka samu da yanzu za ku hadu yanzu za ya aminta da kai ku yi mu’amulla har ya sakar ma ka da jikin sa ya ba ka amana. Yardar sa ta sa harshen sa ya ke saurin yaduwa kamar wutar bazara.

Amma a yau, Malam Bahaushe ya na neman zama malalaci, abin kyama ma saboda ya gurbata al’adar sa da halayyar sa.

Kai!, tir Subhana, Allah dai wadaran naka ya lalace, wai bauna ta ga sa ya na huda. Ni dan boko ne, wanda ma ya ke daga gaba-gaba. Kuma duk inda na je a Duniya na tabbata za a iya jera ni a cikin sahun ‘yan boko, amma ina kyamar halayen wasu ‘yan boko na Kasar nan. Shi ya sa galiban na ke kasancewa bakauyen dan boko. Ni dai ba zan iya ba matata mota in ce ta ja ta rika shiga tsakanin maza ta na kece raini ba. Ka ga a nan, gaba daya an tashi daga zancen aurantaka, kasancewa mace ta amshi sadaki da niyyar za ta zauna a karkashin naimji shi ne ikon ta, shi ne shugabanta, shi ne cin ta shi kuma ne shan ta da ma muhallin ta. Ga kuma mata da rauni don Allah Ya halicce su ba su kai maza tunani da hankali ba. Daga ranar da aka ce an sakar ma mace ragamar gabatar da harkokin rayuwa to an bani an lalace, zaman lafiya ya fara karanci. Idan dai mun kira kawunan mu musulman kwarai to kada mu manta cewa Sayyidina Aliyu (AS) ya taba kiran ‘yar say a tambaye ta ‘shin minene mafi alkhairin diya mace a rayuwa’? Sai ta bas hi amsa ta ce: ‘ta zauna cikin dakin ta ta kebanta da kowa kada ta fita sai da larura mai kwari’. Sai Aliyu (AS) y ace mata ‘kin yi daidai’ Dadin karawa kuma lokacin da aka kasha Sayyidina Usman bin Affan sa’llin kalifancin sa sai A’isha matar Annabin Rahama (SAW) ta fito ta hau bias rakumi ta nufi filin daga don ta daukar masa fansa, da ya ke ‘yar uwarsa ce. Mi ya faru ? Sai Sayyidina Ali ya tarbe ta ya ce ta sauko domin ‘sirdi ga ‘ya mace’ haramun ne (Ma’ana babu kyau mace ta yi sirdi ta hau bisa mota ko mashin ko doki ko rakumi sai dai fa inda wani muharramin ta. Da ta ki sauka ko ta koma sai ya zare takobi y ace za ya sare ta, ganin haka sai ta yakice nikabi don ta san ba za ya ga fuskar ta ba, sai ya juya. Itama ta juya ta koma. Wannan ya nuna haramun ne mace ta tuka abin hawa. Amma mazan mu ‘yan boko da mata ma’aurata sun gaza gane haka. Sai kulluma ce ana so a yi koyi da koyarwar Manzon Allah (SAW) da khalifofin sa.

Abin da ya jawo wannan zance ko rubutu shi ne da kwanan nan mata: jawarawa da matan aure da ma ‘yammata mazauna birnin Katsina su ka fara hawan mashin sun a tukawa da kan sus u na zuwa harkokin su. Na sani cewa tsakanin Nijar da Katsina dududu tafiyar nisan kilomita 90 ne amma ai akwai bambancin al’ada da addini da tarbiyya, na daga Turawan da su ka rene mu (Najeriya da Nijar) Su, Turawan Faransa su ka rene su, sun shiga cikin su sun zauna sun kuma kwace masu addinan su da al’adunsu da salon zamantakewar su kai har ma da tattalin arzukan su. Mu kuma Najeriya Turawan Birtaniya su ka rene mu, sun nuna mana mulkin ‘sassauci’ domin bas u zauna cikin mu bare su nuna mana al’adun su da addinan su ba. Domin tun zuwan su Sarakunan Arewa sun yarda sun amshe su amma sun gindaya masu sharudda na cewa ba za su raba mu da addinan mu da al’adun mu ba. Wannan shi ne kashedin Sarakunan mu ga colonial Masters.  Don bahaushe mai karambanin saurin kwaikwayon al’adun wani ne, don haka ina ganin kwanan nan matan mu za su fara tuka babura.

Don haka, a yau addinin musulunci ba gaba dayan sa ake yi a kasashen da su ke karkashin renon Faransa ba. Kai, bari in yi ma zancen tsirara. Zina ba wani abin laifi ba ne a kasashen renon Faransa. Shi ya sanya mace na iya tafiya ta kwana ko ta tare a dakin saurayin ta ko ta gayyace shi ya zo gidan su ya tare ya yi ta yin zina da ita. Alhali ga dakin ta ga na uwarta. Mutanen renon Faransa kwata ba su damu da yin shiga da ta dace da al’adar Malam Bahaushe ba, gas hi sun lalace kamar Turawa. Lalacewar a kasar Nijar da Benin da Togo da Chadi da Cot’de buwa da Barkina Faso ta kai kololuwa ta inda a yanzu maza da mata na iya yin rawa kusan tsirara ma a bainar mutane.

Wani bukin gargajiya na shekara-shekara a Damagaran, cikin Maris 2017 inda maza da mata ke rawa su na kwaikwayon ‘yan Fim na Kano.

Daga inda Malam Bahaushe ya fara lalacewa ya fara barin al’adar sa ta na lalacewa sai lokacin da ya fara barin matar sa na yawon banza a cikin mota. Tuni a cikin birnin Katsina ‘yan boko maza su ka sakar ma matan su motoci su na tukawa su tafi kasuwanni da gidajen kawaye ko dauko yara makaranta. A karkashin wannan shegantaka wadda ba ta dace da macen tsari ba, muddin an so a bi yanda musulunci ya zo da shi, komi mace na iya aikatawa don na fadi tun a sama cewa mata na da raunin Imani. To na yarda da wannan, cewa maza sun kwaikwayi turawa sun lalace sun bar mata na yawo sakaka kamar tumaki. Kada fa a manta cewa kwarya tagari ta na ragaya, in ji diyan Bawo. Amma dadin kari, wata sabuwar shegantakar kuma da ke neman kunno kai a cikin birnin Katsinar Dikko a yau shi ne mata sun fara hawan Babura. Ka ga dama ita rayuwa haka ta ke. Idan tururuwa ta tashi lalacewa sai ta yi fikafikai. Watau tari ya tado ciwon hakarkari. A da a baya, hukuma ta ki daukar mataki akan yawon banza na matan aure, to yanzu abin ya girma, ya gawurta, ya rikide yanzu yawo ake yi a kan mashin.

A kullum a cikin kasuwar Central Market ta cikin birni nan mata ke baje kolin su da marece su yi ta parking da motoci dauke da ‘ya’yan sus u na shiga kasuwa yada yammaci. Su caba ado su kure adaka, su yi kwalliya ta fitar hankali. Idan ka na nesa da su ka na jin kamshin turaren da su ka kwarara ma suturar su. Wasu bas u ma yin shigar kirki da za ta rufe masu al’aura. Abin dai ga shi nan ba tsari. Da muna yin hira da wani mai shago a cikin kasuwar, ina fada masa damuwa ta akan al’amarin sai ya fada mani cewa ai ban ma ga abin takaici ba sai su ke ganin abin haushi. Ya ce mace ko da matar aure ce, idan ta shiga shago sayayyar sutura (ballantana bangaren ‘yan gwanjo) to sai ta tube kayan da ta ke sanye da su ta gwada wadannan da za ta saya ko da kuwa a gaban mai shagon ne. To ina lalacewar da ta fi wannan? Duk mi ya kawo haka? Sakamakon barin koyarwar Annabi (SAW) na cewa mace kada ta fita sai da muharramin ta ma da kuma ba matan motoci su tafi duk inda su ke so. Hadarurrukan da ke tattare da ba mace mota ta fita yawo su na da yawa in da za a tona. Na kuma taba kai mota ta gareji gyara watarana a cikin Katsina. Mu na zaune da bakaniken sai na ga ana ta bugo masa waya ya ki dauka. Can dai na kasa daurewa na ce masa ya amsa wayar mana. Sai ya yi tsaki ya ce wata matar aure ce ke damun sa da waya, cewa a nan garejin su ka saba ta na kawo motar ta gyara. To kuma hakanan kawai sai ta kira shi ta rika neman sa da maganganun banza na batsa. Shi kuma ba ya so. Sai na tambaye shi shin ina mijin ta? Sai ya ce mani mijin ta ya na Legas kuma soja ne, ba ya ma dawowa Katsina akalla sai bayan wata 4. Ga shi ko da yaushe ya na aiko mata da kudi ta na yin bukatu, ga mota ya ajiye mata. Ka ga sai inda mai ya kare. Wani lokaci ma ta kan kira shi a waya da dare ta rika ce masa ya zo gidan ta ya tama ta fira sai ya ki.

Don girman Allah (SWA) don girman fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (SAW) da Alkur’ani mai tsarki matan aure ku rike iyakar muhallin ku, ku daina tsallake shinge.

Mu na fata maza ma’aurata za su kula.

Mu kwana nan.

Exit mobile version