Balarabe Abdullahi" />

Hauwa El-Yakub Ta Shawarci el-Rufai Da Ya Yi Taka-tsantsan Wajen Nadin Mukamai

An tunatar da gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, na ya yi taka-tsantsan na nau’in mutanen da zai nada su a mukamai daban-daban, domin a sami mutanen da su ke da kishin al’umma da kuma jihar Kadunan bakidaya.
Shugabar mata a jam’iyyar APC a karamar hukumar Zariya, Hajiya Hauwa Hassan El-Yakub, ta baya da wannan shawarar a lokacin da ta zanta da wakilinmu, na yadda ta yi karatun baya na wadanda gwamnan jihar Kaduna ya nada su mukamai a shekara hudun da ya yi a farkon mulkinsa a jihar Kaduna.
Hajiya Hauwa Hassan ta ci gaba da cewar, mafiya yawan wadanda gwamnan jihar Kaduna ya nada mukamai manya da kuma kananan mukamai, mutane ne da babu abin da ke cikin zuciyarsu, sai tunanin me za su samu a gwamnatin da kuma yadda za su yi su gina kan su, ba tunanin al’ummar jihar Kaduna ba.
A nan ne Shugabar mata a jam’iyyar APC a karamar hukumar Zariya, ta nanata cewar, nada mutane da suke da hali irin na gwamna El-Rufa’i, shi ne kawai zai zama alheri ga al’ummar jihar Kaduna, kamar yadda ta ce, mutanen da gwamnan ya nada ne za su aiwatar da kyawawan tsare-tsaren da gwamnan ya saw a gaba, da za su ciyar da jihar Kaduna da kuma al’ummar jihar gaba, kamar yadda gwamnan ya ke da shi a cikin zuciyarsa a shekara hudun da suka gabata.
A kuma tsokacin da Hajiya Hauwa El-Yakub ta yi kan zabar mace a matsayin mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, a cewar ta, wannan ya alamta gwamnan jihar Kaduna na da kyawawan tsare-tsare, da za su tallafa wa rayuwar mata a jihar Kaduna, musammam in an dubi yadda mataimakiyar gwamnan ta yi ayyuka da dama a baya, kafin ta zama mataimakiyar ghwamna a jihar Kaduna a zaben day a gabata.
Ta kara da cewar, mafiya yawan matan da gwamna ya nada su mukamai a daga shekara ta 2015 zuwa shekara ta 2019, mata ne da ba su tallafa wa mata ba, a wasu lokuta ma in mata sun je wajensu, sais u rika cewar, su ba ‘yan siyasa ba ne, cewar ba zabensu aka yi ba, ka da ‘yan siyasa su dame su, ta tabbatar da cewar, in aknada ‘yan siyasa tare da wadanda suke da tunanin al’umma a zukatansu, ba za su furta ire-iren wadannan kalamai ba.

Exit mobile version