Connect with us

FITATTUN MATA

Hauwa Hussain Muhammad: Lura Da Azabtarwar Da Makota Ke Wa Yara Ya Sa Ta Zama ‘Yar Gwagwarmayar Kare Hakkinsu

Published

on

Ko-Kun-San

Hauwa Hussain Muhammad ita ce shugabar gidauniyar nan mai fadi tashin kare ‘yancin mata da yara da kuma yaki da cin zarafinsu mai suna ‘Fighting Against Woman And Child Biolations’, haka kuma ita ce mataimakiyar shugaban babban makarantar sakandari na  G.I.S.S da ke Yolawa. Ta kasance mace mai yunkuri a kowani lokaci domin yaki da cin zarafin mata, wannan kokarin nata ne ma ya sanya ta shiga jerin fitattun mata domin ta yi nasarori sosai musamman ta fuskacin samar wa yara hanyoyin ilimi da kuma kare ‘yancin wasu mata, musamman wadanda suke ciki halin kunci, ta jure kalobale sosai a kan wannan sa’ayin.

Hauwa ta sha samun lambobin yabo da jinjina kan kokarinta na kare mutuncin yara da mata, domin ko a shekata ta 2016 Gwamnan Jihar Kano da hadin kungiyoyi masu zaman kansu sun karramata da lambar yabo mafi girma a dukkanin fadin Kano tana daga cikin mata uku rak da aka zaba domin basu wannan lambar yabo, da maza goma  a shekara ta 2016 kan kare mutuncin yara da mata, wanda wannan lambar yabon ya yi gayar fito da ita duniya ta santa.

Wace ce Hauwa Hussain Muhammad?

An haife Hauwa Hussain ne jihar Kano a ranar 1 ga watan Junairu, 1973. Ta fara karatun Firamare dinta ne a Brigade Special Primary School a 1986, sai kuma ta gangara makarantar  mata na Woman Teachers College da ke Kano, inda ta yi karatunta a kan fannin ilimin koyarwa (Satifiket NCE) a shekara ta 1991, ta kuma sake halartar makarantar horar da malamai da ke Kano (F.C.E) inda ta samu shaidar karatun ilimin koyarwa  (N.C.E) 1991. bayan nan Hauwa ta halarci jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ta samu shaidar karatun digiri a fannin ilimi (B.ED education) ta kuma kammala ne a shekara ta 2004.

Hauwa’u ita ce mukaddashiyar shugaban makarantar sakandari na G.I.S.S da ke Yolawa, kafin zamanta mataimakiyar shugaban babban sakandarin, ta fara aiki ne a ma’aikatar ilimi a jihar a matsayin malamar firamare a makarantar musumman da ke Jakara Special Primary tun daga 1990 ba ta jima sosai a wannan makarantar ba, sai ta sake samun aiki na dindindin a matsayin malamar makaranta a firamare na musamman da ke Dandago Special Primary daga 1994 har zuwa 2007 wanda ta taka matakai sosai a wannan janibi, daga bisani kuma ta sake sauya wajen aiki zuwa babban makarantar sakandari na G.G.S.S Sani Mainagge a matsayin malamar makaranta, sai kuma aka yi mata canjin wajen aiki zuwa makarantar sakandari G.G.A.C da ke Goron Dutse, Kano zuwa shekara ta 2014, har wala yau an mata sauyin wajen aiki zuwa sakandarin G.G.A.S.S da ke Kofar Na’isa Kano, a shekara ta 2016. A halin yanzu kuma ita ce mataimakiyar shugaban makarantar sakandarin Yolawa.

Ta ina Hauwa ta shahara?

Hauwa ta samu shiga cikin jerin fitattun mata ne a sakamakon kasancewarta mai fadi ta kare ‘yancin mata da yara da kuma yaki da cin zarafin mata, ta samu nasarori sosai a wannan janibin, a bisa haka ne mata ta kafa wata kungiya mai aikace-aikacen yaki da cin zarafin mata da yara mai suna  ‘Fighting Against Woman And Child Biolations’, ita ce ta assasa wannan kungiyar ta kuma kasance shugaban kungiyar, haka kuma ta samu nasararori da jinjina masu tarin yawa a bisa kokarinta a kan kare ‘yanci da cin zarafi mata da yara. Bayan wannan, Hauwa ita ce mataimakin shugaban kungiyar nan da ke wayar da matasa da kuma hada kansu ta hanyar kafafen sadarwa. Ita ce jami’ar hulda da jama’a na kungiyar mata masu sana’o’i a Jihar Kano, haka mamba ce a cikin kungiyar nan na marubuta ‘Mace Mutum Writers Association’, haka kuma ita Hauwa tana daga cikin mata masu kare ‘yancin jama’a ‘Human Right Network’, ita mamba ce a cibiyar da ke bada lambar yabo mai daraja ‘Crystal Prestigious Award’.

Wani tagomashi da Hauwa Hussain ta samu a rayuwar, ita ce mace ta karshe wato (‘yar auta) ita kadai ce ta samu zarafin yin karatu tun daga firamare har zuwa sakandari har zuwa jami’a a cikin ‘yan uwanta mata, hakan kuma ya biyu bayan yanayin da suka samu kansu na raino a wajen kakansu, wanda shi bai sha’awar karatun boko, amma cikin ludufin Allah ya kubutar da Hauwa ta samu zarafin yin karatu. Ranar da baban Hauwa ya shaida mata ya amince mata da ta yi karatun boko a firamare ta yi ta tsalle domin murna, hakan na nuna mata burinta zai cika kenan, domin kakansu ya ki lamunce wa kowace ‘ya mace ta yi karatun boko. bayan rasuwarsa ne Hauwa ta fara zuwa makaranta a kashin kanta tun bata ma san amfanin karatun ba. ta dai yi nasara, domin mahaifinta ya mara mata baya tun a wancan lokacin.

Ko mene ne ya sanya Hauwa ta tsunduma kare ‘yancin mata da yara?

Ta samu kan a jerin masu kare cin zarafin mata da yara ne a sakamakon yanda ta taso ta ga yanda ake cin zarafin yara a duniya, da fari dai ta ga yanda wata makwafciyarsu ta dinga azaftar da yarinyar riko da aka bata ne, domin matar takan sanya yarinyar talla da kuma dukarta da dai yi mata abubuwan da basu dace ba; wannan dalilin ne ya sosa wa Hauwa’u rai, tun daga wannan lokacin ne ta fara ganin lamarin a kaikaice, haka ita kanta Hauwan bayan da mahaifinta ya rasu an mika rikonta a hanun yayarta a lokacin ta ga banbancin raiyo wadannan dalilan suna daga cikin abubuwan da suka dami Hauwa tun lokacin da take kuruciya. Bayan da Allah ya sa ta girma kuma, kasantuwar yanayin karatun da ta karanta na ‘social studies’ ta sake nazarin yanda ake rage wa mata ‘yancinsu da zalumta musamman ta fuskacin kin sanya su karatu da sauran cin zarafin mata. Ta fuskacin yara kuma, Hauwa ta sha yin karanbanin sanya yaran da suke hayo sakaka a kwararo da kuma almajirai a makarantar boko, wani lokacin ta yi nasara wani lokacin kuma a fi karfinta a kwace yaran, wani lokacin a barta ta ci gaba da kula da karatun yara, ta yi irin wadannan abubuwan da daman gaske wanda kuma ta yi nasarori, irin wadannan burin nata ne ta kafa gidauniyarta na kanta mai yaki da cin zarafin mata da yara.

Ko ta samu cimma wasu nasarori a wannan yaki da cin zarafin mata

Hauwa ta cimma nasarori sosai, amma daga cikin nasarorin da ta cimma wanda ya daga lifafarta ta calla ne a duniya, akwai wata matar da take cikin kuncin rayuwa da yaranta a wani lokaci a sakamakon gallaza mata da mijinta ke yi, abun ka da mai neman taimako, Hauwa ta bibiyi matsalolin matarta, wani lokaci ta je gidan rediyo ana hira da ita sai take bayyana cewar ga wani abun da ke damunwata ko Allah zai sanya a samu masu taimakawa, cikin ludufin Allah aka kirata a wayar tarho aka nemi ta kai su gidan da wannan matar ke ciki domin a taimaka mata, babbar nasarar Hauwa matar nan ta fita daga cikin kangin rayuwa kuma ‘ya’yanta  shida 6 dukka sun samu zarafin yin karatu sosai. Sai kuma wani nasara da ta cimma sai kuma wata matar aure da mijinta ya yi sanadiyyar haukacewarta a dalilin yawaita yi mata dukan fitar hankali, ya kuma ki ya bada damar a kaita jinya da kuma shigar da ‘ya’yanta makaranta, wannan gidauniyar na Hauwa ta yi hubbasawa a yanzu haka wannan matar sun yi nasarar kaita asibitin muhaukata ana dubata, ‘ya’yanta kuma an sanyasu a makaranta duk da mijin ya ki amma sun fi karfinsa da hujjoji da kuma neman ceto rayuwar ‘ya’yansa da matarsa. Irin wadannan suna da yawa wanda gidauniyar Hauwa ta iya cimmawa. A bisa irin wadannan aikace-aikacen na Hauwa’u Hussain ne ya sanya ta samu lambobin yabo masu tarin yawa daga kungiyoyi masu zaman kansu da kuma gwamnatin jiharta ta kano, ko a baya bayan nan tana daga cikin zakaru mata uku da aka karrama kan yaki da cin zarafin mata a yara a jihar Kano 2016, wanda gwamnatin jihar ta yi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: