Dr. Ojji Dike, wanda kwararren masanin cutar da ta shafi zuciya a asibitin koyarwa na Jami’ar Abuja, ya bayyana cewar, cutar Hawan Jini ce sanadiyar mutuwar mutane kashi 20 a duniya.
Dike ya bayyana hakan ne lokacin da ake aiwatar da tsarin kula da kasancewa ba tare da Teba ba, na shekara- shekara, wanda ofishin sakataren gwamnatin tarayya na kasa, ya shirya ranar Alhamis ta makon daya gabata a Abuja.
Kamar dai yadda bayanin nashi ya nuna shi al’amarin Hawan Jini wadda cutar cardiobascular ne, shine yake kasancewa sanadiyar mutuwar mutane masu yawa a duniya.
Cardiobascular wata cut ace wadda ke zama sanadiyar toshewar ko kuma tsukewar hanyoyin da jini yake tafiya, hakan kuma yana iya kasancewa sanadiyar, bugawar zuciya, ciwon kirji, ko kuma mutuwar bangaren jiki.
Sauran matsalolin sun hada da matsalolin da suke shafar naman da yake tare da zuciya, da dai sauran wasu matsalolin kamar, balbes ko kuma rhythm wadanda suma suna daga cikin cututtukan da suke nasaba da zuciya.
Ya bayyana cewar bayan shafar zuciyar da ita cutar ta cardiobascular har ila yau tana shafar Koda, ita kuma ce jagora, wajen samar da cutar mutuwar wanisashe na jikin mutum, saboda cutar tana hana jini tafiya zuwa wurin daya dace na jiki.
“Fiye da kashi 20 na mutane aduniya suna mutuwa ne a sanadiyyar cutar matsalolin da suke nasaba da zuciya, sai kuma mutuwar mutane kashi 22 a nahiyar Afirka, ya yin da kuma kasar Nijeriya, a gabashin kasar fiye da kashi 40 na mutane ne suna mutuwa a sanadiyar ita cutar.
“Dalilan da suke sun hada da wadanda aka sani da kuma wadanda ba a sani ba.
“Da akwai dai na farko wadanda suka hada da shekaru, jinsi, tarihin iyalai, suna daga cikin abubuwan da ba za, a iya canza su ba, wato wani ba zai iya canza su ba, amma dai kawai za a iya lura da yadda shi al’amarin yake.
“Ta wani bangaren kuma da akwai wadansu abubuwa wadanda suma su kan kasance sanadiya, sai dai kuma su wadannan mutum yana iya daukar mataki, kamar Hawan Jini, sinadarin cholesterol mai yawa, Kiba da kuma cutar Sikari.
“Rashin motsa jiki, shan Taba Sigari, ga kuma shi al’amarin daya shafi shan Giya ko kuma Barasa mai yawa kamar dai yadda shi Dike ya bayyana”.
Don haka sai ya yi kira da wadanda suka halarci taron cewar, su rika zuwa ana duba lafiyar su da irin halin da take ciki, da kuma gwada jinin su yake, da kuma duba shi yadda mizanin cholesterol yake, da kuma yadda mizaanin sikarin su yake.
Kwararre kuma masanin cututtukan da suke nasaba da zuciya, ya bayar da shawar a rika yin motsa jiki akai -akai, sai kuma rage nauyin jiki, ko kuma kiba, ga kuma al’amarin daya shafi cin abinci mai nagarta wanda ya kunshi dukkan nau’oin abincin da suka kamata, wadanda kuma daga karshe ake kiran su balace diet. Ga kuma samun isasshiyar hutawa, inda kuma ya ce, babban mutum yana bukatar yin hutu, sai kuma yin barci na a kalla awa shida ko wacce rana. hutawa ta a kalla awa shida .
Mista Olusegun Adekunle wanda babban sakatare ne a ofishin Sakataren gwamnatin tarayya shima ana shi jawabin, ya bayyana cewar, dole ne mutane su kasance masu motsa jikinsu ne akai- akai, su kuma rika zuwa asibiti ana duba halin da lafiyarsu take ciki.
Ya yi kira da ma’aikatan da suke ofishin cewar su rika tafiyar da rayuwa mai tsafta, sai kuma su ci abinci mai kyau, da kuma yin amfani da kayayyakin da ofishin. ya tanadar.
Adekunle ya nuna rashin jin dadin shi akan yadda mutane basu kulawa da jikinsu, sai kuma sun bari wadansu abubuwan da basu da kyau sun faru gare su tukunna, daga baya kuma su nemi taimako.
Mrs Maria Rufa’i ita darekta ce ta bangaren daya shafi al’amurar ma’akata, ta bayyana cewar, shi tsarin dalilin dya sa aka bullo da shi ko kuma taken shi taron shine, `Lafiyar jiki da kuma kasancewa ba,a cikin matsalar kiba ba” abin an shirya shine saboda a a wayar da kan ma’aikatan ofishin Sakataren gwamnatin tarayya ta kasa, amfanin kasncewa cikin lafiya da walwala.
“Al’amarin daya shafi wayar da kan ma’aikatan ofoshin, akan amfani da shi taken al’amarin daya shafi abubuwan da suka kamata mutum ya rika yi ma lafiyar jikin shi. Ya kuma daina yin halin ko in kula akan al’amarin daya shafi lafiyar shi.
Ya cigaba da bayanin cewar “Duk mun sa kayayyakin da suka kamata kai har ma da asibiti, duk dai abinda ya kamata bai wuce, a rika amfani dasu kada a bata su, saboda an kashe kudade masu yawa.”
Kamfanin dillanci labarai na Nijeriya ya bayyana rahoton shi tsarin na kula da lafiya, Ofishin Sakataren gwamnatin tarayya ne ya shirya shi, cewar, ana kuma yin shi shekra- shekara, saboda a kara wa ma’aikata kwarin gwiwa suna ba lafiyar jikinsu lokacin kulawa da shi.