Hawan Jini Ya Na Saurin Kisa In Ba A Nemi Magani Akan Lokaci Ba –Masani

Hawan Jini

Shugaban sashen magani na asibitin ‘Living Standard’ dake garin Benin, ya ce cutar hawan jina ta na iya jawo saurin mutuwa, in har mutum bai nemi magani ba a kan lokaci.

Dakta Jide Owolana ya bayyana hakan ne a yayi da yake ganawa da manema labarai yau Litinin a garin Benin, Likitan ya ce hawan jini ba shi da wani takamaiman alamu da ke nuna an kamu da ciwon, amma in aka gano shi to ayi magani akan lokaci, in kuma ba haka ba, to zai iya haifar da ciwon zuciya, da shanyewar sashen jiki, da ma mutuwa.

Hawan jini yana faruwa ne a daidai lokacin da karfin jini da yake gudana ta jijiyar mutum, yafi karfin jijiyar, rahotonni sun nuna akalla mutum miliyan 1.5 me suke fama da hawan jini a Nijeriya, duk da masana sun ce ana iya gadon cutar.

Hanya mafi dacewa na magance cutar itace, aje a ziyarci kwararrun likitoci don su auna mutum, sannan su rubuta mishi maganin da ya dace, sannan mutane su kiyaye shan magunguna da ba likita bane ya rubuta musu, saboda yin hakan na da matukar hadari ga lafiyar dan Adam.

Wasu daga cikin dalilan da suke haifar da hawan jini sun hada da tsufa, tsarin rayuwa, kiba, tsarin cin abinci, rashin motsa jiki, da kuma yawan amfani da gishiri, wasu dalilai na daban sun hada da shan taba sigari, rashin barci isasshe, gado, da kuma yawan kwakwadan giya.

Exit mobile version