Abba Ibrahim Wada" />

Hazard Malalacin Dan Wasa Ne, Cewar Mikel Obi

Tsohon dan wasan Najeriya John Obi Mikel, ya bayyana dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Eden Hazard, a matsayin malalacin dan wasan da bai taba gani ba a kwallon kafa.
Obi Mikel dai sunyi wasa tare da Hazard a kungiyar kwallon kafa ta Chelsea a baya na tsawon shekaru kuma yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka shaku da dan wasa Edin Hazard kafin yabar Chelsea din.
Kwarewar da Hazard din ya haifar shine ya sa ya sami damar komawa Real Madrid a bana, amma yadda yake buga wasa a filin wasa na Santiago Bernabeu ya janyo ce-ce-ku-ce game da ingancin lafiyarsa.
Sai dai ana ganin dan wasan dan asalin kasar Belgium zai iya nuna bajinta idan aka kwatanta yadda yake buga wasa a Chelsea din a baya kuma ya koma sabuwar kungiya da sabuwar kasar da kuma sabuwar gasa.
‘Hazard yana da baiwa ta ban mamaki musamman yadda yake sarrafa kwallo sai dai watakila ba shi da kwarewa kamar [Lionel] Messi, amma yana iya yin duk abin da ya ga dama ya murza kwallo” in ji Obi
Ya cigaba da cewa “Ba ya son karbar horo mai tsanani yayin da muke karbar horo abinda ya yi fice akai shi ne tsayuwa yana kallon mu amma a ranar lahadi ya bada mamaki kwarai, domin rawar da ya taka abin a yaba masa ne, ni kaina ya bani mamaki.”
Kawo yanzu dai duka Mikel Obi da Edin Hazard din basa buga wasa a kungiyar Chelsea sai dai a lokacin da suke bugawa kungiyar kwallo sun taimaka mata wajen lashe kofin firimiya da gasar FA da kuma kofin lig Cup.

Exit mobile version