Abba Ibrahim Wada" />

Hazard Na Dab Da Komawa Real Madrid

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid tana dab da daukar dan wasa Edin Hazard bayan da tattaunawa tayi nisa tsakanin Real Madrid da Chelsea yayinda tuni Hazard din ya amince da albashin da zai dinga karba idan ya koma.

Tun bayan kammala gasar cin kofin duniyar da aka kammala a shekarar data gabata aka fara danganta dan wasan da komawa Madrid din sai dai Chelsea ta dage cewa bazata siyar da dan wasan nata ba.

Hazard dai ya zura kwallaye 19 sannan ya taimaka an zura kwallaye 12 cikin wasanni 44 daya bugawa kungiyar a wannan kakar sai dai kuma kwantaraginsa zai kare a karshen kakar wasa ta gaba wanda hakan yasa Chelsea take ganin zata hakura ta siyar dashi.

Kamar yadda rahotanni suka bayyana a kasar Sipaniya Real Madrid tana dab da kammala siyan dan wasan bayan da ta amince zata biya abinda Chelsea take bukata sai dai har yanzu ba’a bayyana kudin ba.

Wasu rahotanni sun bayyana cewa kafin Zidane ya amince da dawowa kungiyar sai da sukayi yarjejeniya da kungiyar akan cewa dole sai an siyo masa Edin Hazard kuma shugaban kungiyar ya amince da hakan.

Tuni dai akayi waje da Real Madrid a gasar cin kofin zakarun turai da ake fafatawa a wannan shekarar kuma akwai tazarar maki 12 tsakaninta da Barcelona a gasar laliga har ila yau kuma Barcelona ce tayi waje da ita  a gasar cin kofin Copa Del Rey.

Exit mobile version