Connect with us

WASANNI

Hazard Zai  Iya Kai Matsayin Ronaldo Da Messi

Published

on

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, Ceser Azplicueta ya  bayyana cewa dan wasan kungiyar, Edin Hazard zai iya kai matsayin da Ronaldo da Messi suke na zura kwallaye a raga idan har ya ci gaba da dagewa.

Hazard dai ya fara buga gasar firimiya ta wannan shekarar da kafar dama bayan ya zura kwallaye biyar a wasannin daya buga a kungiyar ciki har da kwallaye ukun daya zura a ragar kungiyar Cardiff City a satin daya gabata.

Dan wasan ya ci gaba da cewa koda ace Hazard bai iya zura kwallaye kamar na Ronaldo da Messi ba amma zai iya zura kwallaye masu yawa sakamakon wahalar da gasar firimiya take dashi musaamman a ‘yan shekarun nan.

“A wannan kakar yana zura kwallaye a raga sannan kuma yana taimakawa ragowar ‘yan wasan kungiyar suma suna cin kwallo saboda haka muna fatan wannan shekarar za ta zama shekararsa a duniya bama a firimiya ba” in ji Azplicueta

Ya ci gaba da cewa “Messi da Ronaldo suna zura kwallaye a raga kusan 50 a kakar wasa guda daya hakan yasa babu dan wasan da yake iya kaiwa matsayinsu amma idan Hazard ya ci gaba da zura kwallaye kuma yana taimakawa zai iya kamosu”

Ya kara da cewa Hazard shine babban dan wasan kungiyar Chelsea amma kuma duk da haka baya jin kansa saboda babba ne kuma yana girmama kowanne dan wasa kamar yadda shima ake bashi girma.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: