Abba Ibrahim Wada" />

Hazard Zai Samu Duk Abin Da Yake So A Real Madrid – Fabregas

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa t achelsea, Cech Fabregas, ya bayyana cewa idan Hazard ya cigaba da zama a kungiyar ta Chelsea bazai iya lashe kowacce irin kyauta ba a rayuwarsa amma idan ya koma Real Madrid yanada damar lashe kyaututtuka iri-iri.

A ranar Laraba dai Hazard ya bayyana cewa yayi bankwana da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea bayan da suka doke Arsenal a wasan karshe na cin kofin Europa wasan da dan wasan ya zura kwallaye biyu a raga.

Real Madrid dai ta bayyana aniyarta ta siyan dan wasan wanda ta dade tana zawarci kuma a daidai wannan lokaci ya amince da albashin da kungiyar zata bashi yanzu ciniki ya rage tsakanin Chelsea da Real Madrid.

“Ina ganin wannan shine wasan karshe d azan bugawa kungiyar Chelsea sai dai daman babban burina shine mu lashe kofin Europa saboda munsha wahala kafin mu kawo wannan mataki kuma mun gama aikinmu” in ji Hazard

Ya ci gaba da cewa “Ina mika sakon godiya ga magoya baya da ‘yan uwana ‘yan wasa da mai koyarwa da kuma duk wanda ya kasance a wanann kungiya wadda take cikin manyan kungiyoyin duniya”

“Hazard dan wasa ne wanda ya iya buga kwallo kuma ya dade a Chelsea saboda haka akwai bukatar yabar kungiyar domin komawa wata kungiyar daban sai dai ba na son mutane suyi zaton kamar ina adawa da Chelsea ne” in ji Fabregas

Ya ci gaba da cewa “Ina tunanin ba zai iya lashe kowacce kyauta ba a Chelsea kuma dan wasa ne wanda yakamata ace yana lashe kyauta irin wadda Ronaldo da Messi suke lashewa amma akwai kungiyoyin da sunansu da tarihinsu yafi na Chelsea kuma idan yaje zai samu abinda yake so”

Exit mobile version