Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home DAGA BIRNIN SIN

Hedkwatar Majalisar BCI Ta Yi Biris Da Rahotanni 2 Da Ofishin Wakilinta A Shanghai Ya Gabatar Da Ke Tabbatar Da Cewa Babu “Aikin Tilas” A Xinjiang

by Sulaiman Ibrahim
March 28, 2021
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Hedkwatar Majalisar BCI Ta Yi Biris Da Rahotanni 2 Da Ofishin Wakilinta A Shanghai Ya Gabatar Da Ke Tabbatar Da Cewa Babu “Aikin Tilas” A Xinjiang
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga CRI Hausa

Kwanan nan, wasu kamfanonin kasashen waje kamar su H&M da Nike sun yi ikirarin cewa, wai ana samun matsalar “aikin tilas” a jihar Xinjiang, kuma sun bayyana kin amfani da kayayyakin audugar kirar Xinjiang, sanarwar da suka bayar ta jawo hankalin jama’a.
A ‘yan kwanakin da suka wuce kuma, shugabannin wasu kamfanonin auduga a Xinjiang su ma sun nuna cewa, tun shekarar da ta gabata, an soke duk takardun oda na fitar da kayayyakin auduga da aka riga aka sanya hannu ba zato ba tsammani. Me ya sa audugar Xinjiang take fuskantar matsaloli?
A watan Agustan shekarar 2020, Majalisar Ci Gaban Auduga Ta Switzerland (BCI) ta ba da sanarwar soke takardar shaidar tabbaci ga duk kamfanonin auduga na Xinjiang har sai abin da hali yayi. Wannan mataki ya sanya kayayyakin audugar Xinjiang sun shiga cikin jerin sunayen da aka haramta musu cinikin kasa da kasa bisa dalilinta na wai kamfanonin audugar na Xinjiang suna fama da matsalar “aikin tilas”. Game da haka, ‘yan kasuwar auduga da ma’aikatan kamfanonin auduga na Xinjiang sun karyata shi.
Me ya sa majalisar BCI ta yanke irin hukunci dake sabanin gaskiya? Wannan na faruwa ne da karyar da wasu kafofin watsa labarai na yammacin duniya suka kirkiro a cikin ‘yan shekarun nan.
Tun daga shekarar 2019, wasu kafofin watsa labarai da kungiyoyi masu zaman kansu na kasashen yamma, ciki har da su Cibiyar Nazarin Manufofin Dabarun Australiya, da kafar watsa labarai ta BBC, da kuma jaridar Wall Street da dai sauransu suna ta yin zargin cewa, wai ana fama da matsalar “aikin tilas” a jihar Xinjiang, har ma suna mayar da masana’antun auduga ta Xinjiang a matsayin “yankin da aka tilastawa aiki sosai”.
Domin ba da amsa kan ra’ayoyin jama’a na kasashen waje game da maganar “aikin tilas”, ofishin wakilin BCI a Shanghai ya kara gudanar da cikakken bincike kan ayyukansu a Xinjiang kuma a karshe ya tabbatar da cewa, babu wani abu mai kama da “aikin tilas” a jihar. Sun gabatar da rahotanni biyu na binciken ga hedkwatarsa, sannan kuma sun tattara rahotannin binciken na wasu hukumomin bincike kamar SGS ta Switzerland suka bayar a ‘yan shekarun da suka gabata. Amma, hedkwatar BCI ta yi biris da rahotannin tantancewar da ofishin wakilanta na Shanghai da Hukumar SGS suka gabatar, ta ce, akwai matsalar “aikin tilas” a kamfanonin auduga na Xinjiang, kuma babu wani dalili na soke takardar shaidar “Kyakkyawan Auduga” da ta baiwa masana’antun auduga na Xinjiang har abada. A sakamakon haka, audugar Xinjiang kusan tan 500,000 ba za su iya shiga tsarin samar da kayan auduga na kasa da kasa ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

SendShareTweetShare
Previous Post

Sin Tana Da Karfi Da Aniyar Mayar Da Martani Kan Matsin Lamba Da Wasu Kasashen Yammacin Duniya Suka Yi Mata

Next Post

Sin Ta Sanar Da Kakaba Takunkumi Kan Wasu Amurkawa Da ‘Yan Kanada Da Wasu Hukumominsu

RelatedPosts

Tsohon Ministan Kudin Girka: Jari Da Sin Ke Zubawa A Afirka Ya Zamo Muhimmin Tallafi Sama Da Mulkin Mallaka Da Kasashen Yamma Suka Yi A Nahiyar

Tsohon Ministan Kudin Girka: Jari Da Sin Ke Zubawa A Afirka Ya Zamo Muhimmin Tallafi Sama Da Mulkin Mallaka Da Kasashen Yamma Suka Yi A Nahiyar

by Sulaiman Ibrahim
6 hours ago
0

Daga CRI Hausa Tsohon ministan kudin kasar Girka Yanis Varoufakis,...

Ya Kamata Nahiyar Afrika Ta Dauki Darasi Daga Annobar COVID-19

Ya Kamata Nahiyar Afrika Ta Dauki Darasi Daga Annobar COVID-19

by Sulaiman Ibrahim
7 hours ago
0

Daga Fa’iza Mustapha Har yanzu duniya na ci gaba da...

Manufar Wariyar Launin Fata Ta Amurka Na Keta Hakkin Dan Adam

by Sulaiman Ibrahim
13 hours ago
0

Daga CRI Hausa A shekarar 1962, marubucin kasar Amurka, ‘dan...

Next Post
Sin Ta Sanar Da Kakaba Takunkumi Kan Wasu Amurkawa Da ‘Yan Kanada Da Wasu Hukumominsu

Sin Ta Sanar Da Kakaba Takunkumi Kan Wasu Amurkawa Da ‘Yan Kanada Da Wasu Hukumominsu

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version