Abba Ibrahim Wada" />

Henry Ya Zama Kociyan Kungiyar Monaco

Daga Abba Ibrahim Gwale

An nada tsohon dan wasan kwallo na gaba na kungiyar Arsenal, Thierry Henry sabon kocin kungiyar Monaco ta Faransa har zuwa shekarar 2021 kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na yanar gizo.

Henry dan kasar Faransa mai shekara 41 da haihuwa ya rike mukamin mataimakin kocin kasar Belgium tun shekara ta 2016 inda kuma sukaje mataki na uku a gasar cin kofin duniya.

Ya fara buga wasan kwallon kafa a kungiyar ta Monaco kuma ya taimaka mata lashe gasar Ligue 1 a shekarar1997.

A yanzu kungiyar na cikin wani mawuyacin hali, domin suna matsayin na uku daga karshe a gasar Ligue 1, matakin da ya sa suka kori kocinsu Leonardo Jardim ranar Alhamis din data gabata.

“Da alama kaddara ta riga fata domin gani na dawo kungiyar da na fara buga wasan kwallon kafa a matsayin kocinta”.in ji Henry

Tarihin Henry

Henry na tare da kasar Belgium a ranar Jumma’a, yayin da suka lallasa Switzerland 2-1 a sabuwar gasar Nations League da hukumar kwallon kafa ta Nahiyar turai.

A watan Yuli ne ya taimaka wa Belgium ta kai matakin kasa ta uku a duniya a gasar cin kofin kwallon kafa da aka yi a kasar Rasha a kwanakin baya.

Ya fara wasan kwallon kafa a Monaco a 1994 a karkashin tsohon kocin Arsenal Arsene Wenger, kafin ya koma Jubentus a shekara ta 1999.

Bayan shekara daya kacal a Italiya, sai ya koma Arsenal inda ya bayar da gudunmawarsa ta lashe gasar firimiya biyu da kofin FA biyu a shekaru takwas da yayi a kungiyar da ke arewacin Landan.

Daga Arsenal sai ya koma Barcelona inda ya lashe La Liga da Copa del Rey da kuma Champions League a kakar wasa daya, wato 2008 zuwa ta 2009.

A shekara ta  2010 sai ya koma kungiyar Red Bulls ta league din MLS a Amurka, inda ya shafe kakar wasa biyar, koda yake ya koma Arsenal na wata biyu a 2012.

Henry ya lashe kofin duniya a 1998 da kungiyarsa ta Faransa, ya kuma lashe gasar kasashen Turai a shekarar 2000 inda a jimilla ya zura kwallo 51 a wasanni 123 da ya buga wa kasarsa.

A watan Disambar 2014 ne yayi ritaya daga buga wasan kwallo, kuma da farko ya fara yin bayanin wasannin kwallo ne a tashoshin talabijin kafin ya koma aikin horaswa da kungiyar Belgium. a 2016.

Exit mobile version