Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Hirar Sadaukarwa

by
1 year ago
in KAUCIN KABA SHA NEMA
4 min read
Sadaukarwa
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Tare Da Hamza Dawaki

Idan a ka ambaci hira, sau da dama abin da ya fi saurin zuwa mana a rai, shi ne duk wani zance ko tattaunawa da mutane za su yi,  a cikin hali irin na nutsuwa ko nishadi. Wato dai wani yanayin tattaunawa a sa rai, kuma wanda ya ake yi sannu-sannu da sakakkiyar fuska. Kai tsaye kenan, ta saba da yanayin ka-ce-na-ce da musu da musayar yawu da dangoginsu, wadanda ake yi cikin daure fuska da daga murya.

Tare da haka kuma, hirar kan bambanta tsakanin rukunan mutane da kuma yanayin abubuwan da ake tattaunawa. Misali, hirar wurin mai shayi, takan kasance cikin daga sauti fiye da wadda ake yi a majalisin karatu, kafin malam ya fito. Kamar yadda hirar wurin daurin aure takan fi ta wurin zaman makoki karfin sauti. Haka nan ne kuma hirar abokai kan fin kaufin sauti, yayin da suke tattaunawa a tsakaninsu, fiye da hirar da daya daga cikin abokan zai yi idan babban yayansa ko mahaifinsa ne yake zantawa da shi.

Labarai Masu Nasaba

Kasancewa Tare

Bayar Da Lokaci

Amma daga cikin hirar da aka  fi kowacce yi cikin sakin fuska da yin kasa-kasa da murya, akwai hirar saurayi da budurwa, wadanda suke tsaka da soyayya. A irin wannan yanayi, kana iya wucewa kusa da su ma, ba ka ji me suke cewa ba, alhali kuma suna maganar. Saboda tsabar sassauta sauti. Ko ka tsaya a kusa da su, ba su san ma ka tsaya ba. Saboda matuka da suka kai wurin bayar da hankali wa junansu. Daya dga cikin kuma manyan abubuwan damuwa a cikin sha’anin masoya, shi ne yadda wannan yanayin hirar tasu yake sauya salo kacokan, bayan sun zama ma’aurata!

Kodayake, yanzu ba dalilin sauyawar wancanyanayin hirar za mu kalla ba, tukun. Abin dai da a farko muke fara so mu kalla, shi ne wancan yanayin hira na masoya guda biyu, kafin su yi aure. Wato hira da ake yi wadda babu wani abu a gefensu da yake dauke musu hankali, t adadi. Kuma mafi yawa, abubuwan da suke tattaunawa, abubuwa ne da suka shafi rayuwarsu, ta wannan fuskar ko ta waccan. To samar da wani yanayi irin wannan a tsakanin ma’aurata, shi ne abin da ake cewa Hirar Sadaukarwa.

A takaice kenan, muna iya cewa Hirar Sadaukarwa, wani yanayi ne da ake samu tsakanin mutane biyu. Da suke tattauna labarun zukatansu, da sauran abubuwan da suka shafe su, wadanda suka shude da wadanda suke ciki da ma wadanda suke tunkaro su. Kuma cikin nishadi da aminci da walwala da sakin rai. 

Dr. Chapman yana ganin, mafiya yawan ma’auratan da suke yawaita korafin cewa abokan rayuwarsu na aure ba sa magana. Ba wai sam ba sa magana ba ne. Suna nufin kawai ba sa bayar da lokacinsu ga abokan zaman don yin irin wannan hira ta  sadaukarwa.  Domin idan yaren matarka na soyayya ya kasance bayar da lokaci ne, to fa zai yi wuya ta iya yarda da gaske kana son ta, matukar dai ba ka ba ta irin wannan dama ta hirar sadaukarwa.

Watakila wani ya ga kamar, hirar sadaukarwa tana da kamanceceniya da wasu gabobi a cikin yaren soyayya na farko da muka gabatar. Sai dai abu ne mai sauki kuma mu iya fahimtar sun sha bamban gaya, ta fuska guda. Ko kuma ma kawai ba su da wata alaka da juna. Domin yare na farko, duk hankali yana komawa ne kan lafuzan da ake fada din. Wato kalmomi ko magana da za ka yi wa abokin zamanka don karfafa masa guiwa, ko kalaman yabawa, ko kyakwawan lafuza da dangoginsu. A wannan yanyi dukka, tasirin yana cikin lafuzan ko kalmomin da za a  ko ake furtawa ne. Amma a nan tasirin yana cikin abin da za ka tsaya ka ji daga bakin abokin rayuwar taka.

A takaice dai, a yare na farko, an fi damuwa da abin da muke furtawa ne. Yayin da a nan kuma aka fi damuwa da abin da muke saurara.

Sabanin wanda yake aika sakon so ta hanyar kalmomin yabo ko kyawawan lafuza, wanda yake aika sokon soyayya ta hanyar bayar da lokaci ko hirar sadaukarwa, ya fi mayar da hankali ga sauraren abin da abokin zaman nasa yake cewa. Wato kenan, yayin da wancan ya dage yana da yabon kyan matarsa ko iya girkinta. Shi kuwa wannan watakila ka same shi yana yi mata wasu tambayoyi a cikin abubuwan da suke burge shi game da sha’aninta. Don kawai ya kara fahimtar ainishin labarin da ke ciki zuciyarta, hangenta da kuma abubuwan da suke burge ta. don haka, watakila kenan, yayin da magidanci na daya ya yi jumloli dari a cikin tattaunawarsa, shi kuma na biyun za ka taras bai fi guda talatin ya yi ba. Saboda wancan magana yake yi, wannan kuma sauraro yake.

Dr. Chapman ya bayar da labarin wani magidanci, wanda sai bayan sun rabu da matar tasa ne ya fahimci ainishin wautar da ya tafka. Ya ce, kullum matar nan tasa in ta dawo daga wurin aiki, sai ta yi masa korafi game da wurin aikin nan nata. Shi kuma kullum ta yi masa korafin sai ya ba ta shawarar yadda za ta dakile wannan matsalar. Amma abin da ya fi bata masa rai, gobe ma in ta dawo sai ta maimaita wannan matsalar ko wata. Har yake ce mata ita fa matsala ba ta magance kanta da kanta, dole sai an tashi an dau matakin dakile ta. Amma matar nan kullum jiya ya yau. Har ma wataran in ta zo tana kara zayyana masa matsalolin sai ya tambaye ta. Kin bi waccan hanyar  ko matakin da na gaya miki ki dauka? Sai ta ce masa a’a.

Don haka daga karshe dai sai ma ya ce mata, to daga yau kar ma ta tsammaci wata tausayawa ko nuna damuwarsa game da matsalarta. Kar ma ta kara fada masa. Tun da duk shawarwarin da ya ba ta ba ta dauka.

Sai daga karshe da kansa yake bayyana irin girman shashancin da ya yi. Domin a lokacin ne, bayan sun rabu da matar, ya fahimci ashe duk wannan korafin da take ta faman yi masa, sam ba ma don ya ba ta shawara ba ne. kacokan ma ba wai kai tsaye don neman mafita daga wannan matsalolin take korafin ba. Babban burinta kawai shi ne, ya ba ta lokaci, ya saurare ta, kuma ya nuna ya fahimci irin gwagwarmayar da ta ke yi, a kalla kuma ya nuna kulawa ko damuwarsa dangane da sha’anin. Amma shi don shashanci, (kamar yadda ya kan ce) ya shagaltu kawai da ba ta shawara.

Idan kuwa za a yi la’akari da koke-koken matan aure yanzu, abu ne mai sauki mu iya fahimtar cewa, kaso mai tsoka daga cikinsu ne suke fuskantar irin wannan matsala. Wato mazan a yawancin lokuta ba sa iya sauraren su, su fahimci damuwarsu, su kuma bayyana musu tasu damuwar dangane da lamarin. Kuma, a wurin macen da yaren soyayyarta ya kasance bayar da lokaci ne, to hakika babu wani abu da mijinta zai yi ma ta ta iya gamsuwa cewa lallai ya na son ta, matukar dai ba ta samu irin wannan damar ba.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Me Ake Nufi Da Ado? Darussa Daga ‘Sociology Of Fashion’

Next Post

’Yan Sintirin Agro Rangers Sun Fatattaki Makiyaya A Oyo Don Hana Rikici

Labarai Masu Nasaba

kasancewa tare

Kasancewa Tare

by
2 years ago
0

...

Lokaci

Bayar Da Lokaci

by
2 years ago
0

...

Kalaman Cusa Kiyayya Da Tasirinsu A Tsakanin Jama’a

Kyakkyawan Lafazi Yaren Kowa Ne

by
2 years ago
0

...

Soyayyar Zamani

Kalmomin Girmamawa

by
2 years ago
0

...

Next Post
'Yan Sintirin

’Yan Sintirin Agro Rangers Sun Fatattaki Makiyaya A Oyo Don Hana Rikici

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: