Idris Umar" />

Hisba Ta Karrama ‘Ya’yanta Da Suka Sami Shiga Aikin Soja Da ‘Yan Sanda

Exif_JPEG_420

A cikin satin da ya gabata ne kungiyar Hisba ta kasa reshen karamar hukumar Sabon Gari dake jihar Kaduna ta karrama wasu yayanta da suka Sami nasarar samun aikin Soja da Dan Sanda da N.Y.S.C a wannan shekarar na 2020.

Wakilinmu na da ya daga cikin wakilan kafar yada labarai da suka sami halartar wannan taro kuma ya bayyana yadda bukin ya wakana kamar haka .

Taron angudanar da shi ne a harabar ofishin Hisba dake Anguwar Muciya dake Sabon Gari Zariya jihar Kaduna.

Bayan manyan baki sun gama zuwa sai aka fara taro tare da kiran wadanda aka shirya taron dominsu.

Daga cikin wadanda aka shirya taron dominsu akwai sojoji guda 2 sai Dan sanda 1 sai NYSC mutum 2.

Malam Muhammad Saminu Umar shine Uban taro kuma shi ne ya jawo hankalin yayan kungiyar da suka Sami nasarar samun wani matsayin a wannan lokacin.

Malamin ya fara ne da godiya ga Allah tare da jinjina ga yayan kungiyar bisa yadda suka nuna dakewa da son ci gaban kasa wanda hakan yasa har suka Sami wannan nasarar.

Uban taron ya nuna matukar Jin dadi ganin yadda kungiyar suka shirya taron don karrama takwarorinsu yace, Allah yayi masu albarka karshe yayi kira ga Wanda suka sami sabbin mukaman da suyi aiki cikin tsoran Allah yace hakan zai sa su sami nasara a rayuwansu baki daya, Kuma yayi fatan Allah ya kawo zaman lafiya a kasa baki daya

Abubakar Lawal Adam shine Kwamandar shiyar ta karamar hukumar Sabon Gari shima a nasa jawabi yayin kammala taron ya nuna farin ciki da ganin wannan rana.

Kwamandar yace dalilin karrama yayan kungiyar da suka Sami nasarar shiga aikin Soja da Dan Sanda da NYSC shine don sun fitar da kungiyar Hisba kunya a kasa baki daya saboda tun da suka shiga tsangayar horo basu guduba wanda hakan ya nuna suna da kishin ci gaba kasarsu Nijeriya tare da yiata hidima a rayuwansu hakan shine makasudin karramasu.

Karshe ya yi kira garesu da su zama jakadu na gari wadda hakan zai sa sauran yayan kungiyar na Hisba su Sami kwarin guiwar ci gaba da bayar da gufummawarsu ga Al’ummar kasa baki daya.

Kuma ya tabbatar da cewa ita Hisba kungiyace dake taimakon kowa da kowa ba lailai sai musulmiba kuma ita take daukar nauyin kanta da kanta wajan gudanar da harkokin yau da kullun ya kuma yi godiya ga dukkan yayan kungiyar da suka bada goyan baya har taron ya Sami nasara.

 

Exit mobile version