Daga Idris Aliyu Daudawa,
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wasu matasa 53 akan zargin da ake masu na aikata alfasha a cikin garin na Kano.
Malam Lawal Ibrahim wanda yake shi ne jami’in hulda da jama’a na hukumar, shi ne wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Kano, ya bayyana cewar an kama su ne akan bayanai na sirri.
Kamar dai yadda ya ce an kama su wadanda ake zargin ne a daren Talata a Lamido Crescent da ke karamar hukumar Nasarawa ta jihar, saboda sayar da miyagun kwayoyi da kuma kayan maye.
“Mutanen mu sun je wurin da misalin karfe 10:00 na dare ne inda suka cafke mutum 53 da ake zargi kamar dai yadda ya yi bayani”.
Ibrahim, wanda ya kara da cewa an tantance wadanda ake zargin yadda ya kamata, ya ce, “mun gano cewa dukkan su sun kasance masu laifi na farko ne. An yi masu nasiha tare da mika su ga iyayensu. ”
Ya ce Kwamandan-Janar na hukumar, Haruna Ibn-Sina, ya gargadi matasa a jihar da su guji rayuwar bata gari su zama ‘yan kasa na gari.
Manema labarai sun ruwaito cewa “haramtattun ayyuka” an haramta su a karkashin dokar shari’a da ke aiki a jihar Kano.