Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Hobbasar Kwazon Tambuwal Na Fara Biyan Albashi Daga Haraji A 2023

by Muhammad
January 24, 2021
in RAHOTANNI
4 min read
Kwazon Tambuwal
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,

Gwamnatin Jihar Sakkwato a karkashin jagorancin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ta jajirce tare da daura damarar rage dogoro da kudaden Gwamnatin Tarayya ta hanyar fitowa da hanyoyi da dama na bunkasa haraji domin tsayuwa da kafafun ta.

A yayin da Jihohi da dama ke kasa iya rike kan su, rashin aiwatar da ayyukan raya jiha da kuka da ma’aikata ke yi kan rashin tsayayyen albashi da bin bashin albashin watanni da sauran hakkoki; a nata bangaren Gwamnatin Jihar Sakkwato ta sha albashin zama Jiha ta farko a Nijeriya da za ta fara biyan albashi daga harajin da ta ke karba a 2023.

A shekaru da dama zuwa yau kwararru, masana da shugabanni da dama sun yi ta nuna bukatar fitowa da hanyoyin bunkasa haraji domin dogaro da kai maimakon dogaro kacokam da kudaden kason wata-wata daga asusun Gwamnatin Tarayya (FAAC) A cewarsu ba yadda za a yi a samu ci-gaban tattalin arziki idan Jihohi ba su tsayu da kafafun su ba.

Tallafi daga Asusun Gwamnatin Tarayya a shekarar da ta gabata zuwa ga Jihohi 36 da Birnin Tarayya Abuja ya kama naira tiriliyan 4.4 wanda aka samu daga kudaden Haraji wanda naira tiriliyan 1.3 ne a shekarar 2019 wanda ke nuna Jihohi sun dogaro da kudaden ne da kashi 70.5% kamar yadda rahoton Economic Confidential ya nuna tare da cewar idan babu tallafin Gwamnatin Tarayya ga Jihohi a kowane wata, Jihohi.

da dama ba za su iya dogara da kansu ba.

A kan sha’anin bunkasa haraji, Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayyyana cewar nauyin da ke wuyan Gwamnati yana da yawan gaske. “Muna kashe naira biliyan uku wajen biyan albashi da alawus a duk wata, kuma kudaden haraji da muke samu ba su wuce naira biliyan 4.2 ba don haka yana da kyau mu dauki matakin samar da karin kudin shiga domin akalla a rika biyan ma’aikata albashi.” In ji Gwamnan a wani taron wayar da kai kan muhimmancin biyan haraji a watan Maris.

Ya ce “Domin gyara a wannan fannin, mun inganta Hukumar Tattara Haraji tare da samar mata shugabanni nagari wadanda za su gudanar da aikin yadda ya kamata. Ko kadan babu siyasa a sha’anin biyan haraji, siyasa ta riga ta wuce don haka a ajiye ta a gefe a rungumi ci-gaban jama’a.”

“Gwamnati za ta mayar da hankali ga kudaden harajin da ake samu wajen yi wa jama’a ayyuka da su. A karkashin jagorancin mu ba za a samu handama da babakere ba, za mu yi iyakar kokarin rike amanar dukiyar jama’a da yardar Allah.” Cewar Shugaban na Kungiyar Gwamnonin PDP.

A tashin farko, Gwamnatin Tambuwal wadda tun farkon shigarta ofis a 2015, ta fito da sababbin hanyoyin bunkasa kudaden shiga a yanzu haka ta karfafa tare da inganta ayyukan Hukumar Tattara Haraji ta Jiha (SOIRS) ta hanyar sabbin tsare-tsare, fitowa da sababbin dokoki, toshe sulalewar haraji, hada haraji a waje daya, tabbatar da shigar haraji a asusun Gwamnati da daukar sababbin ma’aikata domin ganin kwalliya ta biya kudin sabulu.

Bugu da kari a bisa ga hobbasar kwazon inganta haraji da samar da karin kudin shiga; Gwamnatin Jihar Sakkwato ta kaddamar da shafin yanar gizo da za a rika biyan haraji a saukake ko da daga kwance a gida ne a kokarin da take yi na fara biyan albashin ma’aikata daga harajin da take tarawa a 2023.

“Nan da shekaru biyu Jihar Sakkwato za ta fara biyan albashi a harajin da ke tarawa. Zuwa shekarar 2023, Jihar Sakkwato za ta zama jiha ta farko a Nijeriya da za ta rika biyan albashin ma’aikata daga harajin da take karba na jiha.” In ji Dasuki.

Dasuki wanda shi ne San-Turakin Sakkwato ya ce a bisa ga shiraruwan da suka sa a gaba na bunkasa tattalin arziki suna bukatar Jihar Sakkwato ta ci-gaba da zama kan gaba ta yadda sauran Jihohin kasar nan za su rika koyi da ita.

A kwanan nan ne Jihar Sakkwato ta samu jinjinar musamman daga Bankin Duniya ta hanyar zama ta daya a Nijeriya bakidaya a shirin Gwamnatin Jiha na tsaftace tu’ammali da kudade (SFTAS) ta hanyar kaiwa mataki na 14/15 tare da samun tallafin tsabar zunzurutun kudin naira biliyan takwas wato dala miliyan 22 daga Bankin Duniya kan aiwatar da gaskiya da adalci a harkokin kudade.

Kari da karau a makon jiya Gwamnatin Tarayya ta hannun Ma’aikatar Kudi ta Tarayya ta bayyyana Jihar Sakkwato a matsayin ta daya a kasa bakidaya wajen bin tsarin gaskiya da adalci a harkokin kudade tare da samun tsabar kudi naira biliyan shida 6.612.

Gwamnatin Sakkwato wadda ta samu nasarar toshe badakalar naira miliyan 500 da ke sulalewa a kowane wata daga albashin ma’aikata da gano ma’aikatan bogi sama da 1, 000 a yanzu haka ita ce jiha ta farko a kasar nan da ke biyan albashi kan kari a duk ranakun 23 ga kowane wata ko da kuwa a karshe mako ne.

Jihar Sakkwato wadda ta shiga sahun farko wajen cika ka’idojin huldar kudade na wata-wata da biyan kudaden da ake bin ta bashi a 2019 kamar yadda ofishin Babban Akawun Gwamnatin Tarayya da Ofishin Kula da Bashi na Kasa ya bayyana ta yi nasarar samun Shugaba nagari Aminu Waziri Tambuwal a matsayin Gwamna da kwararren masani harkokin kudi Hon. Abdussamad Dasuki, a matsayin Kwamishinan Kudi wadanda suka daga daraja da martabar Jihar har ta samu yabo da tallafi daga Bankin Duniya tare da daura damarar kai ta a tudun mun tsira cewar Oseni Elemah tsohon Sakataren Hukumar Haraji ta Kasa a jawabinsa kwanan nan a taron Horas da Sababbin Ma’aikatan Hukumar Tattara Haraji ta Jiha a Sakkwato.

SendShareTweetShare
Previous Post

Aminu Alan Waka Ya Yi Bayani Game Da Sarautar Danburan Din Gobir

Next Post

Jami’ar ABU Ta Yi Alkawarin Tabbatar Da Tsaro A Harbobinta

RelatedPosts

ACF

Kungiyar ACF Da Badakalar Jagoranci A Yankin Arewa

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Zailani Bappa, Al’ummar Arewa da dama za su tabbatar...

NLC

Mafi Karancin Albashi: Wata Kungiya Ta Yi Tir Da Kalaman NLC Akan Dan Majalisa Datti Babawo

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Bello Hamza, Wata kungiya mai zaman kanta mai suna...

Abduljabbar

Abduljabbar Bai Kai Darajar A Yi Masa Gangami Ba –Sheikh Khalil

by Muhammad
2 days ago
0

Ya Ce, Dalilin Da Ya Sa Sarkin Musulmi Ya Hana...

Next Post
ABU

Jami’ar ABU Ta Yi Alkawarin Tabbatar Da Tsaro A Harbobinta

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version