Connect with us

LABARAI

Hon. Dasuki Ya Tallafa Wa Masu Amai Da Gudawa A Sakkwato

Published

on

A bisa ga barkewar annobar zazzafar cutar Amai da Zawo a garin Dan-Madi da ke a Karamar Hukumar Tambuwal, Dan Majalisar Yankin, Honarabul Abdussamad Dasuki ya kai agajin gaggawa domin shawo kan lamarin wanda mutane hudu suka rasu yayin da aka kwantar da mutane 20 a asibiti.
Hon. Dasuki wanda ke wakiltar Mazabar Kebbe/Tambuwal kuma Shugaban Kwamitin Sojojin Ruwa A Majalisar Wakilai ya bayar da daukin na gaggawa ne na magunguna, allurai, ruwa da sinadarin tsaftace hannu a jiya na dubban daruruwan kudi.
Bashar Isah Jabo (Sarkin Yakin Jabo) ne ya wakilci Hon. Dasuki ya kuma bayyana alhini da jimamin Dan Majalisar kan barkewar annobar wadda ta girgiza zukatan al’umma tare da jajanta masu kan wadanda suka rasa rayukansu tare da kira gare su kan bayar da muhimmanci ga kula da lafiyar su.
“Mun zo ne kwana da faruwar lamarin domin jajanta muku a kan wannan jarabawa tare da bada taimakon gaggawa domin kawar da wannan matsalar. Muna rokon Allah ya gafartawa wadanda suka rasu, ya baiwa wadanda suka kamu da cutar lafiya ya kuma kiyaye afkuwar hakan a gaba.” Ya bayyana.
Hon. Dasuki ya kuma bayyana cewar idan akwai wata bukata da suke da ita baya ga tallafin da ya kawo masu to su gabatar da bukatar ga kwamitinsa domin kawo daukin da ya kamata.
Da yake jawabi a madadin al’ummar Dan- Madi fitaccen dan siyasa, Hon. Attahiru Umar Dan- Madi ya yi godiya ga Hon. Dasuki kan kawo daukin na gaggawa tare da sayo dukkanin magungunan da asibiti ta bukata domin shawo kan matsalar.
Hakimin Dan- Madi Alhaji Abubakar Zaki ya bayyana jin dadi da kulawar da Dan Majalisar ya nunawa al’ummarsa kan kawo agajin gaggawa a lokacin da ake bukatarsa tare da rokon Allah ya ci-gaba da yi masa jagora, ya kuma ce za su yi amfani da kayan agajin yadda ya kamata.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: