Hon. Dogara Ba Dan Jam’iyyar PDP Ba Ne, Inji Kakakinta

Dogara

Daga Khalid Idris Doya,

Jam’iyyar PDP da ke mulkin jihar Bauchi ta ce, tsohon Kakakin Majalisar Tarayya, Rt. Hon. Yakubu Dogara ba dan jam’iyyar ba ne, inda suka gargadi masu hada hotunan gwamnan jihar Bala Muhammad da na Dogara wanda PDP ta misalta hakan a matsayin neman dagula lamuran siyasa a jihar.

Wannan bayanin wanda ke zuwa a daidai lokacin da jam’iyyar APC ta ce Dogara ba mambanta ba ne, an samu bullar wasu hotuna wadanda aka yada su a jihar Bauchi da ke nuna Dogara da Gwamnan Bauchi dauke da tambarin lemar PDP a jiki.

Jami’in watsa labarai na jam’iyyar PDP a jihar Bauchi, Alhaji Yayanuwa Zainabari, a wani taron manema labarai da ya kira a Bauchi, ya ce sun barranta da hotunan da aka yada kuma suna gargadi ga masu hakan, ya shaida cewar kawo yanzu Dogara ba dan jam’iyyarsu ba ne.

Zainabari ya nuna cewa, PDP ba kara-zube take ba, akwai matakai da ka’idojin fita daga jam’iyyar haka akwai dokoki da ka’idojin dawowa cikinta, don haka ne suka ce muddin Dogara na son dawowa jam’iyyar wajibinsa ne ya bi matakan da suka dace ba yada hotunansa da gwamna ba.

A cewar Zainbari: “Mun wayi gari mun ga wasu ‘yan neman cin abinci ko ‘yan dagajin siyasa su na ta kan manna hotuna na gwamnan jihar Bauchi da Yakubu Dogora (Tsohon Kakakin majalisar tarayya) wanda ya ci zabe a karashin jam’iyyar PDP ba tare da bata lokaci ko wani laifi da jam’iyya ko gwamnati jiha ta masa ba, ya yanke hukuncin fita daga jam’iyyar PDP wanda ya rubuta mana takardar ficewa daga jam’iyyarmu a ranar 24 ga watan 7.

“Kamar yadda kuka sani muna da dokoki ba kara zube jam’iyyarmu take ba. Idan ka fita daga jam’iyya za ka rubuto ta hanyoyin da suka dace; don haka idan kana son dawowa cikin jam’iyyar ma akwai matakai da ake bin su.

“A bisa wannan matakai wanda Rt. Hon. Yakubu Dogara ya bi na ajiye shaidar kasancewa dan PDP tun a watannin baya. Don haka muna shaida wa jama’a cewa hotonan da suke gani masu neman dakula lamura ke mannawa. Amma shi Dogara ba dan jam’iyyar PDP ba ne, ya bar jam’iyyar PDP.

“Lokacin da ya bar jam’iyyar PDP, jam’iyyar a matakin jihar Bauchi mun je kotu saboda muna bukatar kujerarmu da jama’a/al’ummar Dass, Tafawa Balewa da Bogoro suka zabi jam’iyyarmu domin ba Yakubu Dogara aka zaba ba; PDP aka zaba. Don haka muna kira ga jama’an da ba su da aikin yi da suke tallan wadannan hotunan da suke neman kawo hautsini muna kiransu da kakkausar murya da su gaggauta daina hakan domin PDP ba za ta zura ido wasu na mata hawan kawara ba.

“PDP jam’iyyace mai bin doka, ba ka shiga sai da doka, ba ka fita sai da doka, ba ka dawowa sai bisa ka’ida. Bisa hakan muke kira ga masu hada hoton Dogara da na gwamnanmu da su daina su kuma guji fushin PDP duk wanda muka kama da wannan laifin za mu nemi hakkinmu da kuma kokarin bata mana suna na danganta mu da wanda ba dan jam’iyyarmu ba ne,” cewar Zainabari.

Da ya ke maida martani kan furucin da tawagar Lauyoyin APC suka yi a kwanakin baya da suka ce Hon. Dogara ba dan jam’iyyar APC ba ne, Kakakin PDPn ya ce, “Mu wannan ba damuwarmu ba ne, domin bayan da Dogara ya barmu, ya ce ya shiga APC. An yi zaben dan majalisar karamar hukumar Dass wanda shi Dogara din ne ya jagoranci tawagar APC don haka sun zo sun ce Dogara ba dan jam’iyyarsu ba ne, su ta shafa, mu kam muna da shaidun da ke tabbatar da Dogara ya jima da fita daga cikinmu.”

PDP ta yi barazanar kara zuwa kotu kan lamuran da suka shafa Hon. Dogaran domin neman wasu daga cikin ababen da ta ce hakkinta ne.

Zainabari ya nuna cewa PDP ta yi wa Dogara goma-ta-arziki wanda a sakamakon Jam’iyyar yake kan kujerar da yake a yau, amma sai ya watsa musu kasa a ido wajen ficewa daga jam’iyyar, ya nuna cewa a lokacin da ya fitan hakan bai musu dadi ba ko kadan.

Ya ce, idan Dogara ya nemi dawowa cikin jam’iyyar, za su duba su gani ko dawowarsa zai amfanesu ko cutar da su kafin su yanke hukunci a kansa, amma dai kawo yanzu ba su bukatarsa sam-sam.

“Ita jam’iyya kullum kofarta a bude yake, kuma ba ma wanda ya kai matsayi irin na Dogara ba, hatta wanda bai kaishi ba, jam’iyya ba za ta so fitarsa ba, kuma in zai dawo za a ba shi kofa. To, amma fa idan ya zama akwai raini ko wulakanci ko kama-karya, abun da Dogara ya yi wa PDP abu ne wanda na tabbata ko wanda ba dan PDP ba zai yi Allah wadai. Jam’iyya ta maka ciki-ta-maka-goyo, ta kama dukkanin abun da ya dace na karamci amma ba tare da ta maka wani laifi ba ka zo ka fita don haka akwai raini a cikin lamarin kenan,” inji shi.

Exit mobile version