Dan majalisar wakilai na Rano, Kibiya da Bunkure na shirin yin gagarumin tallafi ga Mafarauta da mata zall da matasa a yankinsa.
Hon. Kabiru Alhasan Rurum ya bayyana hakan ne a yayin taron raba tallafi da dan majalisar tarayya na Dala, Hon. Babangida Alhasan ya raba wa al’ummar yankinsa.
Ya ce run daga zuwansa majalisar tarayya ya yi makamancin irin wannan tallafi a bangarori daban-daban domin dama wannan akida ce ta su ta taimakon al’umma.
Hon. Kabiru Alhasan Rurum ya yaba wa wannan kokarin dan majalisar na Dala bisa wannan tallafi data yiwa al’ummar Dala.
Ya ce abubuwa da suke aiwatarwa dama ita ce akidarsu ta bada wakilci mai inganci na taakon al’umma da kawo aiki na cigaban kasa don rage radadin al’umma.
Hon. Kabiru Alhasan Rurum ya yi kira ga wadanda suka amfana daga tallafin na Dan majalisar Dala su yi kyakkyawan amfani da shi wajen bunkasa cigabansu.