Connect with us

RIGAR 'YANCI

Hon. Sharada Na Birnin Kano Ya Raba Tallafi

Published

on

sharada

Jagoran Jam’iyyar APC na karamar hukumar Birnin Kano. Dan majalisar tarayya mai wakilta yankin Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya yi rabon tallafin motoci da babura da kuma kekunan dinki da jari ga wasu daga cikin al’ummar yankin.

Da ya ke jawabi a yayin rabon Dan majalisar tarayyan ya bayyana cewa sun tarune dan cika alkawari da suka dauka na cewa duk kwana 150 su shirya kwarya kwaryar taro da za su hadu su taya juna murna da bitar nasarori da aka samu sannan a sami abinda ya sauwaka a rabawa mutane musamman yan siyasa wadanda suka taimaka wajen ganin samun nasarar shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Ganduje dashi kansa lokacinda yayi takara. Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya raba motoci da mashina da kekunan dinki da kuma jari.

Shi ma a nasa jawabin daraktan yakin neman zabensa Alhaji Abubakar Kingibe ya ce wannan tafiya da su ke ta sha’aban Sharada sun dauko tane akan jahadi ga wadanda su ke kadanda ne mutane su ke yin abinda bai dace ba a shugabancin karamar hukumar Birni.

Ya ce, siyasa magana ce ta yanci wannan jirgi da Sha’aban ke tukawa ita ce tafiya ta Sha’abaniyya a karamar hukumar birnin Kano sabuwa da Allah ne yasan iyakarta.Tafiya ce da su keyi ta jagora wanda yasan hakkin mutane,wanda ya ke dafa madafun iko mutane suyi arziki mutane su ke karuwa ba raguwa ba a cikin harka daya samu dama wacce mutane suka bashi.

Ya ce abinda jagora Sha’aban yayi musu an basu kekuna da babura shima an danka masa mota dankareriya yana fata abinda yayi musu Allah ya ninka masa ya yi riko da hannunsa ya karfafa masa gwiwarsa.

Ya ce arzikin da ya ke cikin tafiyar Sha’aban Allah ne kadai yasan adadinsa saboda niyyar shi jagoran kullum rawar jikinsa idan ya samu abu ya dawo ya dankawa mutane wannan shi ya ke kwantar musu da hankali su ke cewa baza suyi dana sani ba na shiga harkarnan suka kirawo mutane sukace su zo suyita kuma mutane shaidane kan hakan.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: