Ibrahim Muhammad" />

Horar Da Matasa Ilimin Komfuta Za Ta Sama Wa Dubbansu Aiki A Kano – Baban Wapa

Kakakin Majalisar Kansiloli na karamar Hukumar Birnin Kano, Hon. Yusif Baban Wapa, kuma Sakataren kunkiyar Kansiloli na Nijeriya, ya bayyana cewa idan Shugabanni masu rike da mukaman siyasa da mawadata da sauran masu rike da madafun iko a kowane mataki, suka gano muhinmancin horar da Matasa ilimin Komfuta da sauran sana’oi, to hakan zai samawa dubban daruruwa ko Miliyoyin Matasa aikin yi a Jihar Kano dama kasa baki-daya.
Saboda haka, ya kyautu kowane Shugaba ko Mawadaci ya tashi tsaye wajen horar da Matasan Mazabarsa ko Unguwarsa, ko kauyensa, ko garinsa, ko kuma jiharsa, domin kuwa idan kowa ya yi haka, zai zamanto an hada hannu guri guda kenan, daga nan sai cigaba ya samu.
Har ila yau, Baban Wapa ya kara da cewa, idan ka koma shekarun baya kamar 1990, za ka ga cewa Komfuta ma ba kowa ne ya santa ba, amma ga shi yanzu Matasan Jihar Kano, na samun gagarumin cigaba sosai a ilimin na Komfuta da ma sauran fannoni na rayuwa, musamman idan aka yi la’akari da yadda a duk shekara ake yaye daliban da ke ninninka wadanda aka yaye a baya. Babu shakka, wannan abin farin ciki ne da kuma cigaban wadannan Matasa namu.
Hon. Wapa, ya bayyana haka ne a lokacin bikin yaye dalibai 774, wanda Makarantar Horar da Matasa ta Bision technology da ke titin Gidan Zoo, cikin Birbin Kano ta yi, a ranar Asabar din da ta gabata.
Haka zalika, “a matsayinmu na wadanda Allah Ya baiwa mukami, wajibi ne mu cigaba da iyakar kokarinmu na ganin mun taimaka wa Matasa musamman a bangaren karatu da kuma koyon sana’o’i, ta hanyar horar da su sabbin sana’o’in zamani, domin cigabansu da Jihar Kano da ma kasa baki-daya.
Sannan, a karshe ya yaba wa jagorancinsu na jiha, tun daga kan Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, da sauran masu taimaka masa manya da kanana, da jagororinsu na karamar Hukumar Birni, tun daga kan Shugaban karamar Hukumar ta Birnin Kano, Hon. dantata da Jagoran APC na karamar Hukumar Hon. Muntari Ishak Yakasai da dai sauransu.

Exit mobile version