Shekaru hudu da suka gabata, Rita Gabiola wata yarinya ce ’yar shekara 13 da ke bara a titi a garin Lucban na kasar Philippines. Daga wannan lokacin ne wani kamfanin nuna kwalliyar mata ya dauke ta aiki, wanda aka haska ta a wani shirin talabijin, a inda ta sami mabiya sama da 100,000 a man-hajar ‘Instagram’. Duk wannan ya kasance ne a kan dalilin hoto daya tak.
Labarin Gabiola mai ban al’ajabi da ake kira da ‘tsummokara zuwa dukiya’, ya faro ne a shekara ta 2016. A can baya, tana neman sadaka a titunan Lucban, don taimakawa iyayenta wajen biyan bukatunsu. Mahaifinta ya yi aiki a matsayin mai tara shara, mahaifiyarta kuma tana zauna ne a gida tana kula da ita da sauran ‘yan uwanta maza guda biyar.
Babu dayan yaran da yake zuwa makaranta a lokacin, kuma da kyar iyayen ke iya samar da abinci a kan tebur, don haka Gabiola takan fita don rokon canji ko gudummawar abinci. Wannan shine yadda mai daukar hoto dan Philippines, Topher Burgos, ya ganta, wanda ya halarci bikin Pahiyas a Lucban, a watan Mayu 2016.
Kyakkyawar dabi’arta ce ta ja hankalinsa kuma ya saka hotunan ta a yanar gizo, wanda hakan ya canja rayuwar yarinyar gaba daya tare da danna madanni daya wajen loda hoton a yanar gizo.
Shahararru kamar, Miss World Philippines 2015, Danielle Parungao, Miss International Philippines 2014, Bianca Guidotti da Miss Earth 2015, Angelia Ong, duk sun shiga shafukan sada zumunta don yabawa Gabiola mai kyakkyawar dabi’u da fasali na fuska, kuma hakan ya ja hankali sosai ga mabaratan Lucban.
Kafin ta ankara, yarinyar mai shekaru 13 tana hira da ‘yan jarida, yin tallar kayan kwalliya, fitowa a kananan shirye-shiryen talabijin, da kuma zamowa daya daga cikin ‘yan mata da suka kasance a shirin gaskiya na duniya, Big Brother. Sauran abubuwan da ake yiwa Yarinyar Badjao suma sun taimaka ma ta wajen gina rayuwarta a yanar gizo, gami da magoya baya daga kasashen waje, wasu daga cikinsu sun taimaka ma ta da iyalinta da kudi.
A cikin shekarar 2018, Gabiola ta dura wani bidiyo a YouTube wanda ke nuna sabon gidan da ta siya da iyayenta tare da godewa wani Grace Kreutzer, wani masoyin Amurka mai aminci, wanda rahotanni suka ce sun dauki nauyin gina sabon gidan.
Duk da faruwar da ta yi a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, amma ta ci gaba da shahara a kafofin sada zumunta na Philippines, musamman Instagram, inda take da mabiya sama da 100,000. Tana bayar da rahoton har yanzu tana yin kwalliya lokaci-lokaci, amma a halin yanzu tana fafutukar neman iliminta ne.