Connect with us

DAGA BIRNIN SIN

Hoton Bayan Jikin Mahaifin Shugaba Xi Jinping

Published

on

Kafin shekaru 42 da suka gabata, shugaban kasar Sin Xi Jinping wanda ke karatu a jami’ar Tsinghua ya je lardin Guangdong gudanar da aikin bincike a lokacin hutu tare da mahaifinsa Xi Zhongxun.

Hoton bayan jikin mahaifinsa ya shiga idon Xi Jinping, wanda yake tunatar da shi tunanin bautawa jama’a a cikin ‘yan shekarun da suka gabata. Marigayi Xi Zhongxun ya kawo babban tasiri ga shugaba Xi Jinping bisa hallayar nagartarsa, shugaba Xi da mahaifinsa suna sauke nauyin dake bisa wuyansu yayin da suke bautawa jama’ar kasar da suke kauna matuka.

Yin gyaran fuska da kirkire-kikire

A watan Agustan shekarar 1978, Xi Zhongxun ya je gundumar Boluo ta lardin Guandong gudanar da rangadin aiki.(Wanda ke tsayawa a tsakiyar gefen gabashi ne Xi Jinping)

A ranar 23 ga watan Fabrairun shekarar 2017, Xi Jinping yaje rangadin aiki a sabon yankin Xiong’an na gundumar Anxin ta lardin Hebei.

Yin aiki ba rana ba dare

Xi Zhongxun yana rangadin aiki a wani kamfanin dake lardin Guangdong domin kara fahimtar yanayin samar da kayayyaki da yin gyaran fuska da yake ciki.

A safiyar ranar 11 ga watan Fabrairun shekarar 2018, Xi Jinping ya je kallon iyalin Jielie’eamu wanda ke fama da talauci a kauyen Sanhe na garin Sanchahe na gundumar Zhaojue ta yankin Liangshan na kabilar Yi na lardin Sichuan na kasar.

Cike da imani

Xi Zhongxun ya halarci babban taron da aka kira domin tabbatar da tsaron sansanin Yan’an dake lardin Shaanxi na kasar.

A ranar 31 ga watan Oktoban shekarar 2017, Xi Jinping da sauran zaunannun mambobin hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS sun sake yin rantsuwar halartar Jam’iyyar a dakin tunanin babban taron JKS karo na farko dake birnin Shanghai.

Kaunar al’ummun kasa

Xi Zhongxun yayi zantawa da mazauna gundumar Haikang yayin da yake aiki a lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

A ranar 3 ga watan Nuwamban shekarar 2013, babban sakataren JKS Xi Jinping ya tattauna da jami’ai da manoman kauyen Shibadong dake yammacin lardin Hunan na kasar Sin.
A cikin wata wasikar da Xi Jinping ya rubutawa mahaifinsa, ya bayyana cewa, “Kai kamar wani tsohon bijimi ne, wanda ke shan aiki ba dare ba rana domin bautawa jama’ar kasar Sin, duk wadannan suna kara karfafa mini gwiwa yayin da nake kokarin bautawa jama’ar kasar.”Tsokacin da Xi Jinping yayi ba ma kawai ya nuna kaunarsa ga mahaifinsa bane, har ma ya nuna kaunarsa ga daukacin al’ummun kasar Sin baki daya. (Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: