Hua Chunyin: Ya Zama Wajibi Amurka Ta Yiwa Duniya Cikakken Bayani

Daga CRI Hausa,

A baya bayan nan ne wasu cibiyoyin kasar Philippines, suka gabatar da jerin sanya hannu na hadin gwiwa ga hukumar lafiya ta duniya WHO, suna masu bukatar hukumar ta binciki asalin cutar COVID-19 a cibiyar gwaje gwaje dake Fort Detrick ta Amurka.

Game da hakan, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Sin Hua Chunying, ta ce ya zamewa Amurka wajibi, ta yiwa duniya bayani dalla dalla kan wannan cibiyar bincike da tuni aka rufe ayyukan ta.

Hua Chunying, wadda ta yi wannan tsokaci a taron manema labarai da ya gudana a Talatar nan, ta jaddada kiran da Sin ta jima tana yiwa Amurka cewa, ta gaggauta sauraren damuwar da sassan kasa da kasa ke nunawa kan wannan batu. Kaza lika Sin na fatan Amurka za ta wallafa alkaluman gano bullar wannan cuta a cikin gidan ta, kana ta gayyaci kwararrun WHO, zuwa cibiyar Fort Detrick, da sauran wasu dakunan gwaje gwajen kwayoyin halittu sama da 200 mallakin Amurka dake kasashen waje, da kuma jami’ar North Carolina. (Mai fassarawa: Saminu daga CRI Hausa)

Exit mobile version