Huddersfield Ta Shiga Zawarcin Ahmad Musa

Kungiyar kwallon kafa ta Huddersfield Town ta bayyana aniyarta na siyan dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Leceister City, Ahmad Musa bayan dan wasan tauraruwarsa ta haskaka a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Kungiyar kwallon kafa ta Fulham ma dake kasar Ingila ta nuna sha’awarta na siyan dan wasan yayinda kuma itama tsohuwar kungiyarsa ta CSKA Moscow wadda yake zaman aro daga Leceister City tana neman siyansa gaba daya.
Kungiyar kwallon kafa ta Huddersfield Town dai ta bayyana aniyarta na siyan dan wasan kuma tuni tafara shirin kai tayin kudi domin ganin ta siyi dan wasan wanda ake zaiyi tsada sakamakon kokarin da yayi a gasar cin kofin duniya.
Kungiyar kwallon kafa ta Leceister City dai ta bayyana cewa duk kungiyar da zata siyi dan wasan sai ta biya fam miliyan 16, adadin kudin data kashe lokacin data siya daga kungiyar CSKA Moscow shekaru biyu da suka gabata.
Ahmad Musa dai ya zura kwallaye biyu ne kacal tun bayan komawarsa kungiyar Leceister City sai dai tun bayan komawarsa aro kungiyar CSKA Moscow ya zura kwallaye 6 cikin wasanni 10 daya buga a kasar ta Rasha.
Ahmad Musa ya taba buga wasa a kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars dake kano da BBB Benlo dake kasar Holland kafin kuma yakoma kungiyar CSKA Moscow a Rasha.
Yanzu an fitar da Argentina da Jamus da suka buga wasan karshe a Brazil a shekara ta 2014 kuma an fitar da su ne a filin wasa na Kazan Arena, filin da Koriya ta kudu ta yi waje da Jamus kasar da ke rike da kofin gasar.
Hakan dai ya tabbatar da kofin duniya ya gagari Messi wanda babu abin da bai ci ba a Barcelona har ila yau zai iya kasancewa wannan ce gasar cin kofin duniya ta karshe ga Messi.
Da kyar Argentina ta tsallake zuwa zagaye na biyu daga rukunin D bayan ta samu sa’ar Najeriya daci 2-1 sai dai tun kafin haduwar Faransa da Argentina ake ganin yadda tawagar Messi a Argentina suka sha wahala a wasannin rukuni yana da wahala su iya doke Faransa.

Exit mobile version