Connect with us

RIGAR 'YANCI

Hukuma Ta kwace Gurbatattun Kayan Abinci Na Miliyoyin Naira A Kano

Published

on

Hukumar da ke kare hakkin abinci da ingancinsa tare da hadin guiwa sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki, sun samu nasarar kwace nau’in kayan abinci musamman Maganunuwa na Miliyoyin Naira a Kasuwanni da shagunan JIhar Kano daban daban.

Manajan Daraktan Hukumar Dakta Yusif Muhammad Bichi ne ya bayyana haka cikin wata tattaunawa da akayi dashi a Kano, inda ya bayyana cewa wannan kokari na tafiya kafada da kafada wajen inganta harkokin lura da lafiya da kare barkewar wata annoba a fadin Jihar Kano.

A cewarsa, gurbatattun maganunuwa da kuma wadanda aikinsu ya kare da a ka kama sun hada da Shinkafa, Sukari da sauran kayan cimaka da a ka gurbata ta su, ya kara da cewa mutane sunyi amafani da lokacin rufe gari wajen gudanar da haramtattun kasuwanci, wanda ya bayyana cewa yanzu hukumar a shirye take domin hada kai da sauran masu ruwa da tsaki domin zakulo haramtattun kasuwanci da ake gudanarwa a Jihar Kano.

Haka zalika a wani ci gaban kuma al’ummar karamar Hukumar Bichi sun jinjina wa kokarin Manajan daraktan Hukumar lura da ingancin abinci bisa kokarin da ya ke wajen kula da ‘yan Jam’iyya musamman al’ummar, inda ya fito daga karamar Hukumar Bichi, kamar yadda kungiyar masu rajin yayata kyawawan manufofin Gwamnatin Dakta Abdullahi Umar Ganduje wadanda ke bibiyar kyawawan manufofin wannan Gwamnati, inda suka bukaci ya kara jajircewa domin ganin an samu gagarumin cigaba a zangon Gwamna Ganduje na biyu akan karagar Mulkin Jihar Kano.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: