Shugaban hukumar Alhazan Najeriya Barista Abdullahi Muktar Muhammad, ya ce idan an duba yadda chanjin Dala zuwa Naira yake kimanin shekaru goma da suka wuce za a ga cewa an samu raguwar kudin aikin hajji ne ga Alhazan na Najeriya. Barista Muktar wanda ya shaida hakan lokacin da ya ke yi wa manema labarai karin bayani a Abuja.
Ya ce, baya ga Jakar Alhazan da wasu sauran lamuran aikin hajji da Dala a ke biyan su, ya ce, “kashi casa’in da takwas lissafi ne akan Dala, kudin masauki a Makka, kudin masauki a Madina, kudin Sufuri, kudin Abinci, sa kudin shema, duk wadannan abubuwane da ana lissafinsu a kan darajar Dala, shi Alhaji zai bada Naira ne amma Naira za a chanja ta ne izuwa Dala saboda ayi amfani da ita wajen biyan masu hidima, wanda za a biyasu hakkokinsu.
“To idan aka cire kudin jaka ka cire kudin uniform wanda kowacce kasa take yiwa Alhazan ta domin ya basu shaidar yadda za su gane Alhazan su. Da kuma kudin Yello card, da duk wani abu da Alhaji ya ke biya da Naira, sannan a cikin wadannan kudin aikin hajji akwai kudin guziri na Alhajin, Dala dari takwas in ka bugashi zuwa Naira, Naira kusan dubu dari biyu ne da 40.
“Shi wannan kudin Alhajin za a bawa ya zuba a aljihun sa, ya sayi duk abinda yake so, idan ka dauki gundarin menene kudin aikin hajjin? Bai wuce Miliyan daya da da dubu dari biyu ba, misali a shekara ta 2008, abinda Alhaji ya biya kudin Tikiti na jirgi Dala dubu daya da dari bakwai. A lokacin farashin dalar Naira da goma sha bakwai, a bana farshin jirgi zai biya Dala dubu daya da dari biyar, ya ragu da Dala dari biyu. Amma nawa farashin Dala take a yanzu Naira dari uku da biyar.”
Shugaban na hukumar Hajjin yace lura da wannan ragi da aka samu yasa aka sanya hanyoyin da za a rinka tafiyar da Alhazan, wanda zasu rinka samun ragin kudi kimanin Naira dubu Hamtsin da daya. Da haka kuma za a mayar da Alhazai da suka kammala biya kudaden su.
“Daya daga cikin shugaban hukumar Alhazai na jahohi lokacin da muka yi wani taro yake cewa daya daga cikin Alhazan sa abinda ya kakare masa ya cika kudin Naira dubu Hamtsin, yana mishi albishirin cewa an rage dubu Hamtsin da daya, sai yace masa to bari zai aika masa sa Account ya tura masa sauran dubu dayan sa. To wannan ragin yayi tasiri kwarai da gaske kuma nuna fatan su shugabanni na Saudiyya Allah ya saka musu da alkairi.
“Su kuma Alhazai Allah ya karfafa musu niyyan zuwa kuma ya basu ikon biyan wannan kudin, Allah ya kai kowa lafiya ya dawo dasu lafiya Ameen.”
Daya daga cikin hukumomin agajin Alhazan Salisu Muhammad, yace mun shirya domin fara aikin hidima ga maniyatan, “Najeriya akwai mutane daban-daban akwai ‘yan birni akwai ‘yan kauye, wani ma tun daga Rugarsu bai taba zuwa ko’ina ba irin wadannan suna bukatar a taimaka musu. Saboda za a dauko mutum daga jihar su zuwa sansanin Alhazai.
A na sa ran ranar goma ga watan nan za a fara aikin hidimar Alhazai daga jihar Katsina kuma a ranar sha biyar ga watan za a rufe kammala biyan kudin aikin hajjin.