Hukumar Bunƙasa Fasahar Halittu Za Ta Wadata Kauyuka Da Lantarki

Daga Sulaiman Ibrahim,

Hukumar bunkasa fasahar kere-kere ta kasa (NABDA) ta ce za ta samar da wutar lantarki ga al’ummomin karkara ta hanyar injinan sarrafa sinadarin kayayyakin cikin gida.

Farfesa Abdullahi Mustapha, Darakta Janar na NABDA, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a ranar Alhamis a Abuja, cewa hukumar za ta yi hakan ne tare da hadin gwiwar hukumar samar da wutar lantarki ta karkara (REA).

“Muna gab da rattaba hannu kan wata yarjejeniya ta fahimtar juna (MoU) tare da Hukumar Wutar Lantarki ta karkara, inda za mu yi amfani da injinmu wajen kawo wutar lantarki da iskar gas ga al’ummomin karkara, ” in ji Mustapha.

Ya yi bayanin cewa fasahar zatayi amfani da gurbatattun abubuwa, sannan a sarrafa su zuwa abubuwa masu amfani – kamar kashin saniya zuwa iskar gas da wutar lantarki.

A cewar Mustapha, sashin kere-kere na muhalli na NABDA ne ya kirkiro fasahar.

“Wannan fasaha ce ta cikin gida, fasahar mu; wannan shine abin da muke samarwa, kuma abin da zamu iya bayarwa.

“NABDA na fito da wasu dabaru da za su magance mafi yawan kalubalen da muke fuskanta a kasa, ” in ji shi, ya kara da cewa fasahar za ta kawo ci gaba ga al’umma.

Shugaban na NABDA ya sake nanata cewa babban alhakin hukumar ne amfani da bincike da ci gaban fasahar kere -kere don inganta dukkan bangarorin ci gaban kasar.

Exit mobile version