Daga Abubakar Abba, Kaduna
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC shiyyar jihar Kaduna ta gurfanar da wani mai suna Paul Ehiemau da take zargin kwararren ne wajen damfara.
Paul, an gurfanar dashi ne a gaban Alkali Darius Khobo na Babbar kotun jihar ranar Talata, bisa zargin damfara ta naira miliyan goma sha biyar.
Hukumar ta gurfanar da Paul ne tare da kamfaninsa mai suna Blackrock Trading Logistics da ake zargin da shi ne yake gudanar da damfarar.
Ya yi karyar cewar, shine yake wakiltar kamfanin na STOJ Oil da Gas cewar kamfanin ne, ya ba shi damar gudanar da cinikayya.
Wadanda ake zargin su biyu, sun amsa laifin nasu. Lauyan Hukumar Sa’ad Hannafi Sa’ad ya roki kotun da ta sanya don yanke wa wadanda ake tuhuma hukunci, da kuma tura su gidan kaso ajiya.
Mai kare wadanda ake zargin M.A Shariff ana nashi jawabin, ya yi duk iya kokarinsa don neman a bada belin ta hanyar fadi da baki wadanda ake zargin amma Alkalin kotun yaki amincewa da hakan, inda ya umarci lauyan da ya rubuta a rubuce.
Lauyan ya nemi belin ne, a ka uzurin cewar wanda ake zargin na farko Paul, bai da lafiya, inda ya roki kotun da ta ajiye shi a kurku har zuwa ranar da za a saurari bukatar belin nasa. Alkali Khobo ya bukaci lauyan da gabatar wa da kotun shedar takardar cewar Paul bai da lafiya, inda kuma lauyan ya kasa gabatar da takardar.
Alkalin ya yanke hukuncin da a kai Paul ajiya a gidan yari har zuwa ranar sha tara ga watan Satumbar shekarar don sauraron takardar bada belin.