Hukumar EFCC Ta Gargadi Masu Amfani Da Na’urar ‘POS’ Kan Gurbatacciyar Hada-hada

Daga Mahdi M. Muhammad

Hukumar nan da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), a kwanan nan ne ta gargadi masu gudanar da hada-hadar kudi da wayoyi na banki da ake da kira da na’urar ‘POS’ kan su guji yin cinikayyar kudi ba bisa ka’ida ba.
Shugaban shiyya na hukumar a Sakkwato, CDS Bawa Usman Kaltungo a ranar Alhamis 25 ga Maris, 2021 ya ba da wannan gargadin a wajen wani taro da kungiyar Sakataren kudi ta wayar hannu da Banki, (MMBA), reshen jihar Sakkwato a ofishinsa.
Shugaban na EFCC ya nuna damuwarsa kan yadda ake samun karuwar kudin zamba a cikin kasar, sannan ya yi kira ga kungiyar da ta hada karfi da karfe wajen yaki da safarar kudade da damfarar mutane ta hanyar na’ura.
Amma yayin da yake maida martani game da hakan, mai kula da yankin Kudu maso Yamma na kamfanin na ‘Moniepoint’, Israel Eniolorunda ya fusata da wannan maganar inda yake cewa munanan ayyukan da yawa daga cikin wadannan kamfanonin na POS ke yi a kasar na tura wakilai zuwa ga dandalin su don more ingantattun ayyuka da inganci.
Eniolorunda ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a wajen taron mambobin kungiyar manajojin kamfanin na ‘Moniepoint’ a jihar Oyo a cibiyar taron Maube 21 da ke Ibadan.
A cewar sa, Moniepoint, mai amfanar da kudi ta waya wanda kuma aka sani da kamfanin POS an kiyasta shi a matsayin dandamali mafi inganci, mai saurin gudu da kuma samun riba a Nijeriya.
Eniolorunda ya bayyana cewa, wadatar bayanan da ke kan layi sun sanya kungiyar a matsayin mafi kyawun samar da ayyukan banki ga kwastomomi kamar na sama, sauyin kudi, cire kudi da kuma duk biyan kudi.
Ya kara da cewa, a kimiyance, kimar ta dogara ne akan bayanan da suka nuna cewa ‘MoniePoint’ yanzu yana rufe 35℅ na masana’antar tare da sama da masu aiki 20.
Ya ce, “yunkurin hada-hadar kudi a jihar Oyo da ma kasa baki daya ya samu babban ci gaba tare da kafa kamfanin ‘Moniepoint’ a shekarar 2018.
“Alamar tun daga wannan lokacin ta girma daga karfi zuwa karfi, ta kuma zama jagorar kamfanin dillancin hada-hadar kudade na banki a kasar nan tare da sama da wakilai 30,000 a kowane lungu da sako na kasar da ke sarrafa darajar ma’amala kusan Naira biliyan 400 duk wata,” inji shi.
Da yake magana a kan babban taki na masu gudanar da kamfanin ‘POS’ a karkashin kungiyar a jihar Oyo, Eniolorunda ya ce, “jihar mai saurin tafiya ba shakka tana kan gaba wajen jagorancin masu amfani da wakilai kimanin 3000 tare da darajar mu’amala ta yau da kullum ta kusan Naira biliyan 1.5
“Matsayin manajan rukunin kamfanonin a cikin jihar Oyo a karkashin jagorancin mai kula da jihar, Gboyega Ogunsola ba za a iya bayyana shi ba wajen tabbatar da cewa alamar ta ci gaba da wuce tsammanin kamfanin sadarwar wakilai wajen isar kudi ga wadanda ba su cancanci kudin ba.”
A cewar gudanarwa na Jihar Oyo, Mista Adegboyega Ogunsola, sauran masu gudanarwar na jihar za su yi farin ciki da taron tare da manajan, Tolu Adetuyi da Manajan kasuwanci, Michael Olaitan daga hedkwatar.
Ogunsola ya ce, abin da ya bai wa Moniepoint fifiko a kan sauran masu gudanarwar shi ne Shugaba wanda yake da kwazo kwarai da gaske, kuma wanda ya cusa wa ma’aikatan kwarin gwiwar su sanya kwazo a aikinsu.
daya daga cikin manajan rukuni a Jihar Oyo, Ahmed Ayoade ya bayyana cewa, ingantaccen sabis shine wurin sayar da alama wanda ya sanya Moniepoint mafi kyau dangane da sabis na tallafi na abokan ciniki da kuma saurin amsawa ga bukatun wakilai. Ya kara da cewa, kalubale na nan tafe, amma kungiyar ta shirya tsaf domin shawo kan kalubalen wanda yana daya daga cikin abubuwan da ke sa alamar ta yi fice.

Exit mobile version