Connect with us

LABARAI

Hukumar EFCC Ta Kama Mai Gudanar Da Jami’ar Bogi

Published

on

Jami’an hukumar EFCC, na yankin Fatakwal sun gano jami’ar dake baya da takardar shaida NCE dana Digiri ba tare da amincewar hukuma ba. an kama wanda ake zargin ne a garin Fatakwal ta jihar Ribas.
Ya kafa makarantar ne mai suna “Habana International School of Arts and Science” a shekarar 2017 tare da aboan huldarsa masu suna Monday Nwapi da Misis Justina Okafor.
Suna gudanar da makarantar ne daga wasu cibiyoyi guda biyu a Fatkwal suna yi ne a “Brilliant International Schools” a garin Nsukka kuma suna “Street, Diobu da Paragon Citiy Light College, Agip area.”
Tun da aka kafa makarantar an sha damfara mutane, inda ake bukatar su buya kudaden shiga makaranta dana kudaden makaranta da kudin “project”.
Ana damfarar dalibai ne da cewar makarantar ta “Habana International School of Arts & Science” na da alaka da manyan makarantu 4 ne, da “Abia State College of Education (Technical)” da “Ebenezer College of Education” dake Edda ta jihar Ebonyi da kuma “Enugu State College of Education” sai kuma “Unibersity Of Calabar” dake jihar Kros Ribas. Biniciken da hukumar tayi ya nuna cewar, makarantar “Habana International School of Arts and Science” bata da cikakkiyer alaka da wani makaranta gaba daya.
A shekarar 2008 ne hukumar kula da makarantun ilimi “National Commission for Colleges of Education, NCCE, ta dakatar da duk wata makarantar “FCE” daga mallakar cibiya dake a wajen inda makarantar take zaune.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: