Rahotanni na bayyana cewa jami’an hukumar yaki da rashawa ta EFCC sun cafke tsohon gwmanan jihar Jigawa Ibrahin Saminu Turaki, wanda hukumar ta jima tana kalubalantar sa a gaban kotu sakamakon zargin handame dukiyar jihar Jigawa.
Hukumar EFCC ta tsare tsohon gwamnan jihar Jigawa Ibrahim Saminu Turaki a ofishinta dake Abuja.
A cewar Hukumar, ba za ta saki Saminu ba har sai ranar da za ayi zama na gaba a kotu
domin ci gaba da sauraren karan.