Hukumar farfado da shiyyar Arewa Maso Gabas ta bada kyautar kayayyakin abinci da kuma wasu nau’in ababen more rayuwa domin tallafa wa mabukata na miliyoyin naira ta hannun gidauniyar Jewel Care Foundation domin rabawa ga masu bukatar hakan.
Uwargidan gwamnan jihar Gombe, Asma’u Muhammadu Inuwa Yahaya ca ta amshi kayan tallafi da zimmar tsara yadda za a raba ga wadanda suka dace domin inganta rayuwar talaka ta karkashin gidauniyar nata na Jewel da aka samar domin tallafa wa rayuwar mabukata musamman mata da matasa.
Bayanin hakan na kunshe ne ta cikin wani sanarwar da Bintu Aliyu Sunmonu, Jami’ar watsa labarai ta ofishin matar gwamnan jihar ta fitar, inda ta nuna cewa mabukatar da suke halin neman tallafin rayuwa ne za su ci gajiyar kayan abinci da na more rayuwar.
Da take karbar tallafin, uwargidan gwamnan Hajiya Asma’u ta yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da shirin gwamnatin tarayya na agaji, wanda ta ce ya zo daidai da shirin ta na tallafawa masu fuskantar barazanar rayuwa tare da yaki da cin zarafin mata da rashin daidaiton jinsi a cikin al’umma.
Ta kara cewa, “kungiya ta mai zaman kanta tana kulawa da mabukata tare da samarwa mata da matasa abun dogaro da kai domin sa’ayin ganin rayuwa ta inganta domin samun ci gaba mai daurewa.”
Hajiya Asma’u Yahaya ta kuma yaba wa kokarin hukumar da ta kawo kayan inda ta tabbatar da adalci wajen rabon kayan ga mutanen da suka dace ba tare da nuna son kai ko fifiko ba.
Kamar yadda sanarwar ke cewa, kungiyar matar gwamnan jihar ta Jewel ta dauki tsawon lokaci tana gudanar da ayyukan jin kai da kuma bada tallafi ga rukunin jama’a musamman mata da matasa, sai ta nuna cewa za ta ci gaba da aiwatar da irin wadannan ayyukan domin kyautata rayuwar al’umman jihar Gwambe.
Da ya ke mika kayan ga uwargidan gwamnan jihar Gombe, shugaban hukumar farfado da shiyyar arewa maso gabas, Muhammad Goni Alkali, ya ce, sun kawo tallafin ne don a rage radadin illar annobar cutar Korona a jihar.
Shugaban ya kara da cewar ban da tallafin, sun zo jihar nan don su tattauna da gwamnatin jihar tare da kaddamar da wasu ayyuka dukka domin kyautata rayuwar jama’a.
Shugaban ya taho tare da shugaban kwamitin majalisar dattawa akan hukamar farfado da shiyyar arewa maso gabas da babban Daraktan ayyuka da na jin kai na hukumar, kamar yadda sanarwar ke cewa.
Kayayyakin da aka bayar sun hada da kayan gini, buhunan shinkafa, tabarmai, katifu, taliya dandano, man girki da sauran su.