Connect with us

KASUWANCI

Hukumar FIRS Ta Garkame Asusu 6,772 Na Wadanda Suka Ki Biyan Haraji

Published

on

Shugaban hukumar tara haraji na gwamnatin tarayya (wato FIRS), Mista Tunde Fowler ya samar da cewar, gwamnatin tarayya ba za ta sayar da kayan aka gina da sunan kamfanoni dake fadin kasar nan da ba a biya masu haraji ba.
Mista Tunde Fowler ya sanar da hakan ne a ranar alhamis data gabata a jihar Legas a tarom masu ruwa da tsaki ya ce, har yanzu kasar nan itace ke karbar haraji mafi kankanta a fadin duniya.
Ya ci gaba da cewar, hukumar ta karbo haraji da ya kai naira tirilyan 3.5 daga watan Janairu zuwa Agusta na wanann shekarar, inda ya haura sama da wanda sama da naira tiriliyna daya da aka karaba a 2017.
A cewarsa, abin a rubuce yanada kyau amma abinda nake son in fada shi ne, mafi yawancinmasu biyan harajin da suka biya harajin har yanzu basu canza ba haka dokokin basu canza ba hatta suma masu tuntubar na kamfanonin suma basu canza ba.
Ya yi nuni da cewar duk da farashin mai an yanzu bazai wadaci kasar nan, inda ya ce amma mafita a gare mu itace, a samu bayar da hadin kan da ya dace daga kamfanonin da basu shari sarrafa mai ba.
Ya sanar da cewar, babban fannin da bai shafi mai shi ne shi ne harajin BAT kuma mun gano cewar kamfanoni da dama suna suna karbar BAT amma basa biyan gwamnatin tarayya.
Fowler ya ce hukumar ta gudanar da aikin a cikin kimanin shekara daya akan kayan, inda ya ce mun fara ne daga birnin tarayyar Abuja inda muka gano kadarori sama da 2,000 da kuma filaye da aka gina da sunayen kamfanoni.Farashin kadarorin sun kai naiara tiriliyan biyu kuma masu su basu biya masu haraji ba mun kuma tuntubesu tare da tura masu baya nan mu sai dai wasu suna biya.
Ya kara da cewar, amma wadanda basu biya ba, za mu je Kotu don mu samu amincewar ta don sayar da kadarorin nasu ba kuma a Abuja kawai muke yin aikin ba. A cewarsa, mun kammala da jihar Legas a yanzu kuma muna a jihohin Osun, Oyo da kuma Kaduna a hankali za mu karade kasar nan. Fowler ya ce, hukumar ta kalli dukkan kasuwanci dana yin hadaka asusun kamfanoni da suke samun kaudi da suka kai naira biliyan daya a duk shekara a cikin shekaru uku da suka shige.
Ya yi nuni da cewar dokoki sun gama fayyace komai kafin ka bude asusun kamfani, domin kuwa daya daga cikin bayanan da ake bukata shi ne kana biyan haraji? kuma bankuna 23 da muka yi fashin baki akansu, muna da adadi da ya kai yawan 31,395 daga cikin wanda aka cire wanda ake ganin an maimaita har sau 18,602.
A cewarsa, mun rarrabasu zuwa gida uku wadanda suke da lambar biyan haraji da wadanda basu da lamabar da kuma wadanda basu da lamabar, basa biyan haraji da kuma wadanda suke da lamabr amma kwata-kwata basa biyan harajin.
Ya ce jimlar lambar ta TIN da kuma wadanda basu biya ba, sun kai yawan 6,772.Yaci gaba da cewar ya zuwa yanzu mun tura wasiku 2,980 kuma munyi imanin cewar kafain karshen watan Satumba za mu karbo dukkanin su kuma hakan zai bamu damar kwarin gwiwa don nada bankuna a matsayin wakilan da za su karbo mana kudaden.
Ya bayyana cewar, yawan lambar ta TIN da kuma wanda ba a biya ba sun kai yawan 6,772 kuma za a kulle asusun su na ajiya har sai lokacin da suka kawo kansu. Ya ci gaba da cewar, sun ki zuwa su kawo kansu a shekarar 2016 a saboda haka mun sanar dasu akan hakkin da ya kamata su sauke na biyan harajin su da kuma yin bincike a asusun ajiyar su na banki.
Daga karshe shugaban ya bayyana cewa; “A wannan lokacin bari in nemi gafara domin na tura wasiku kimanin sau biyar na neman gafara domin mun gano cewar irin wadannan kamfanonin sun bude asusun ajiya a banki amma basu sanya lamabar TIN ba kuma sunayen su sun zo nan a saboda haka, ina kira a gare su dasu bayar da hadin kai ga jami’oin banki.”
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: