Daga Bello Hamza,
Shugaban hukumar FRSC ta kasa, Dr. Boboye Oyeyemi ya ce, rundunarsa ta shirya fito da wani tsari na musamman ta yadda za su rage hadurra a manyan hanyoyinmu a cikin wannan shekarar 2021.
Oyeyemi ya bayyana haka ne a taronsa da manyan ma’aikatarsa na farko a wannan shekara wanda aka fara a ranar Juma’a a Abuja.
Ya ce, matakin da suke shirin dauka zai taimaka wajen kawar da dukkan hadurra a hanyoyin kasar nan.
Daga nan ya kuma ce, manyan motoci masu dakon kaya ne ke haifar da lalacewar hanyoynmu, kuma za su dauki dukkan mataki na dakatar da haka.
Ya kuma ce, kasuwanni dake gefen manyan hanyoyin suma suna taimakawa wajen aukar da hadurra a sassan kasar nan haka kuma matafiya da basa bin gadan sama da aka samar don tsallake manyan hayoyi suna aukar da hadurra a kasar nan.
“Hukumar ba za ta yarda barin mattatun motoci akan hanyoyinmu ba don suna taimakwa wajen haifar da matsaloli akan hanyar mu.