Hukumar FRSC Ta Kwace Motoci 373 Marasa Takardu A Kaduna

Hukumar FIRS

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

Hukumar kiyaye haddura ta kasa (FRSC) ta kame motoci 373 dauke da takardun abin hawa da wa’adinsu ya kare, da tsohuwar lamba da kuma wadanda ba su da lasisin tuki a jihar Kaduna.

Kwamandan sashin na FRSC a jihar, Hafiz Mohammed, ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Juma’a cewa, an yi nasarar cafke su ne a yayin aikin hadin gwiwa a Kaduna, Kafanchan da Zariya.

Ya kara da cewa, an kame motoci 252 a Kaduna, 41 a Kafanchan da 80 a Zariya.

Mohammed ya jaddada bukatar masu ababen hawa su yi rajistar motocinsu da kuma mallakar sabbin lamba.

Ya ci gaba da cewa, “har yanzu muna da shari’ar masu motoci da ke dauke da takardu wadanda ba su da rajista, wadanda suka hada da babura masu kafa uku da babura wadanda har yanzu suna bin hanyoyin mu kuma suna aikata laifuka ba tare da an sani ba. Idan aka yi amfani da abin hawa da ke da rijista don aikata laifi, za mu iya gano mutumin ta hanyar shiga cikin rumbun adana bayanan mu, ta amfani da adiresoshin masu keta doka.”

“An bai wa mutane lokaci da za su sayi sababbin lambobin, lasisin tuki da kuma sabunta motocin takardunsu ya kare da bayanai,” in ji shi.

Muhammed ya ce, aikin hadin gwiwar zai dore kuma ya gode wa masu ruwa da tsaki da ke cikin aikin saboda hadin kan da suka bayar.

Exit mobile version